Kada ku ƙara kuɗin sabis – FCCPC ga Multichoice

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Hukumar kare hakkin masu amfani da kayayyaki (FCCPC) ta umarci kamfanin MultiChoice Nijeriya da ya dakatar da ƙarin farashin sabis na DStv da GOtv har sai an kammala bincike kan batun. Wannan umarni ya biyo bayan buƙatar kamfanin na neman ƙarin lokaci kafin bayyana gaban hukumar don kare kansa.

Daraktan hulɗa da jama’a na FCCPC, Ondaje Ijagwu, ya bayyana cewa an amince da buƙatar MultiChoice, amma dole ne su halarci zaman binciken da aka sake tsara ranar 6 ga Maris, 2025. Ya ce ya zama dole kamfanin ya kawo cikakken bayani tare da duk masu ruwa da tsaki.

A cewarsa, hukumar ta umarci MultiChoice da su ci gaba da amfani da tsohon tsarin farashi daga ranar 27 ga Fabrairu, 2025, domin kauce wa cutar da kwastomomi yayin da binciken ke gudana. Ya ce dakatar da ƙarin farashin zai taimaka wajen kare haƙƙin masu amfani da sabis ɗin.

FCCPC ta bayyana cewa za ta ci gaba da sanar da al’umma kan ci gaban binciken da ake yi. Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da masu amfani da DStv da GOtv ke kokawa kan ƙarin farashi a baya-bayan nan.

By ukarofi