
Daga BELLO A. BABAJI
A ranar 1 ga watan Yuni ne Nijeriya za ta fara amfani da Dala miliyan 200 na Gidauniyar bankin Afrexim wajen bunƙasa ayyukan walwala da jin-daɗi da da fasahar ƙiƙira a harkar tattali.
Ministar Al’adu, Hannatu Musa Musawa ta faɗi hakan a ranar Laraba, inda ta ce suna ƙoƙarin amfani da Dala biliyan 2 wajen zuba jari a wasu ƙasashe da ma cikin gida Nijeriya, ta yadda za a samar da ayyukan yi da kuma faɗaɗa harkar tattali a zamanance zuwa Dala biliyan 100 nan da shekarar 2030.
A wata sanarwa da Ma taimaka mata kan shirye-shirye na Ma’aikatar, Jummai Ali ta fitar, Ministar ta bayyana cewa a yanzu haka suna tattaunawa da cibiyoyin kuɗaɗe na ƙasa-da-ƙasa don samun damar zuba jari a ababen da suka dace a ƙoƙarinsu na cimma kayawawan manufofin inganta ƙasa da al’ummarta.
Ta kuma ce, Ministar tana ƙoƙarin tabbatar da hakan ne ta hanyar gudanar shirye-shirye da za su dace da manufofin ajandar Shugaba Bola Tinubu na sabonta ƙasa.
Ta ƙara da cewa, ganin yadda yadda Ma’aikatar ke samar da tsare-tsaren zamani, an samu masu zuba jari, waɗanda a halin yanzu ana tattaunawa da su don ganin an cimma manufar tattali da aka sa gaba a 2030.
