Rikicin majalisar Legas: ‘Yan sanda sun mayar da jami’ai masu tsaron Meranda

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen Jihar Legas ta mayar da jami’an tsaron da aka janye daga ofishin da kuma gidajen kakakin majalisar dokokin jihar, Hon. Mojisola Meranda.

Kwamishinan ‘yan sanda na Legas, Moshood Jimoh, ya sanar da hakan a wata tattaunawa da manema labarai a yammacin ranar Alhamis.

Tun da farko, an janye jami’an tsaron da ke kula da ofishin da kuma gidan Meranda a safiyar ranar Alhamis, lamarin da ya janyo cece-kuce, musamman bayan da aka maido da jami’an tsaron tsohon kakakin majalisar da aka tsige, Hon. Mudashiru Obasa.

Bayan dawowar jami’ansa, Obasa ya isa harabar majalisar tare da sanar da kansa a matsayin kakakin majalisar, sannan ya jagoranci zaman majalisa da wasu ‘yan majalisa ƙalilan suka halarta.

Kwamishinan ‘yan sanda ya bayyana cewa an mayar da jami’an tsaron Meranda bayan kammala tantancewar jami’ai da makaman da ake gudanarwa a faɗin ƙasar.

Ya ce ana gudanar da irin wannan bincike a sauran jihohin Najeriya ba Legas kaɗai ba.

Ana ci gaba da samun ƙarin bayani kan wannan batu.

By ukarofi