Badaƙalar albashi: Gwamna Abba ya dakatar da muƙaddashin shugaban ma’aikatan Jihar Kano

Spread the love

Daga RABIU SANUSI a Kano

Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya dakatar da mai riƙon muƙamin shugaban ma’aikata kuma babban sakatare na Establishment Salisu Mustapha, bisa zargin zarge-zargen da ake yi na yanke albashin ma’aikatan gwamnatin Kano.

Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya aikewa manema labarai a ranar Alhamis.

Sanarwar wadda ta tabbatar da cewa an kuma umurci Salisu Mustapha da ya ajiye muƙamin sa na babban Sakatare na Establishment, a ƙarƙashin ofishin shugaban ma’aikata, don ba da damar gudanar da bincike ba tare da tangarɗa ba.

Sannan kuma Sanarwar ta ƙara da cewa domin tabbatar da ci gaba da gudanar da harkokin mulki, gwamnan ya amince da naɗin Malam Umar Muhammad Jalo, Babban Sakatare na REPA, a matsayin sabon shugaban ma’aikata na riko, har sai an kammala binciken da ake yi.

Gwamna Abba Yusuf ya sake jaddada matsayinsa na ƙin amincewa da almundahanar kuɗi, yana mai gargaɗin cewa duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci mummunan hukunci.

Kwamitin binciken da kwamishina na raya Karkara da birane Abdulkadir Abdussalam ke jagorantar kwamitin da aka ƙaddamar a ranar ta Alhamis, an ba shi wa’adin kwanaki bakwai don gano inda matsalar ta ke tare da gabatar da sakamakon binciken.

Idan za a iya tunawa dai a farkon wannan watan ne aka naɗa Salisu Mustapha a matsayin shugaban ma’aikata na riƙo, biyo bayan hutun jinya da aka baiwa babban shugaban ma’aikatan, Abdullahi Musa, wanda yanzu haka yake jinya a ƙasar Indiya.

By ukarofi