
Hukumar kula da lamuran ilimi a matakin Farko ta Ƙasa (UBEC) ta fitar da jimillar Naira biliyan 44.24 a matsayin kuɗaɗen tallafin daidaito ga jihohi 11.
Rahotanni sun bayyana cewa, jaddawalin raba kuɗin da aka wallafa a shafin UBEC ya nuna cewa jihohin da suka karɓa sun haɗa da Jigawa, Ondo, Taraba, Kogi, Kaduna, Filato, Osun, Zamfara, Bauchi, Sakkwato da Inugu.
An tsara wannan tallafin ne domin taimaka wa kowace jiha da kuma Babban Birnin Tarayya , don samar da muhimman gine gine da ake buƙata wajen aiwatar da shirin Ilimi a matakin Farko na Ƙasa (UBE).
Ana ƙididdige rabon kowace jiha ne bisa adadin kuɗin da UBEC ta samu, kuma ana buƙatar kowace jiha ta bayar da aƙalla kashi 50 cikin 100 na jimillar kuɗin kowane aiki a matsayin nata gudunmawa.
Kuɗaɗen da aka fitar tsakanin watan Janairu zuwa Maris na wannan shekara sun shafi zangon farko zuwa na huɗu na shekarar 2025, sai dai Kaduna ta karɓi kuɗi daga zangon uku na 2024 zuwa zangon huɗu na 2025, yayin da Taraba ta karɓi na shekarun 2024 da 2025 baki ɗaya.
Jihar Zamfara ta karɓi kuɗi na zangon farko zuwa na uku da kuma wani ɓangare na zangon huɗu na 2025.
An fitar da Naira biliyan 3.55 ga kowace daga cikin jihohin Jigawa, Ondo, Kogi, Plateau, Osun, Bauchi, Sokoto da Enugu.
