
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaba Bola Tinubu, ya bayyana cewa ba zai lamunci hayaniya, rashin ɗa’a ko kuma saɓa wa umarnin kotu ba, inda ya jaddada muhimmancin kare dimukraɗiyya da mutunta ɓangaren shari’a ko da kuwa hukuncin bai zo yadda ake so ba.
Shugaba Tinubu ya yi wannan jawabi ne yayin da yake magana da shugabanni da masu haɗa kai na ƙungiyar Renewed Hope Ambassadors, inda ya ce wajibi ne a tsaya tsayin daka akan ƙa’idojin da ke riƙe da ƙasar wuri guda.
“Ba za su tsoratar da ni ba,” in ji shi, yana mai cewa ya sha irin wannan tafiya a baya, kuma a shirye yake ya sake fuskantar ta domin ci-gaban ƙasa”, inji shi.
Ya ƙara da cewa, “Gaskiya ita ce na yi gadon kaina a mulki; marigayi Buhari ni ne, ya kasance abokina a tafiya, kuma na karɓi mulki daga gare shi.”
Kazalika, ya ce “idan ‘yan adawa ba su son ganin fata a hanyoyin da muka gina, a cikin yaran da muka tallafa wa, da kuma tattalin arziƙin da muke haɓakawa, za mu ba su gilashin Bola su kalla da shi. Abu ɗaya da kuke buƙata daga gare ni shi ne alƙawari cewa ba zan gudu daga wannan gwagwarmaya tasu ba”, inji shugaban ƙasar.
