
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
An zargi wasu gungun ‘yan bindiga da kai wa masallata hari a ƙauyen Namama da ke Ƙaramar Hukumar Giwa a Jihar Kaduna yayin da ake tsaka da gudanar da sallar Maghriba, inda suka halaka mutum guda da yin awon-gaba da wasu da dama.
Wata majiya daga yankin da ta gana da ‘yan jarida ta ce, maharan sun kai harin ne a lokacin da ake sallar dare, inda suka harbe wani mutum da sace wasu da ba’a san adadinsu ba.
Ta bayyana cewa, harin ya jefa jama’ar garin cikin firgici da tilasta wa da dama daga cikinsu tserewa zuwa wasu yankuna domin samun tsira daga harin.
Wani mai amfani da kafar X mai suna @Bakatsine ya wallafa cewa, maharan sun kai wa ‘yan garin harin ne yayin da ake tsaka da zabga mamakon ruwan sama.
A cewar rubutun da ya wallafan, wani matashi mai suna Adamu ya rasu a lokacin aukuwar lamarin, yayin da masallata da dama suka jikkata ta samun raunuka.
Har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoto, rundunar ‘yan sandan Kaduna ba ta fitar da wani saƙo na musamman akan al’amarin ba.
