Kaduna: ‘Yan sanda biyu sun rasu bayan farmakin ƴan bindiga a Zangon Kataf

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Wasu gomman ƴan bindiga a garin Zonkwa da ke Ƙaramar Hukumar Zangon Kataf na Jihar Kaduna, sun farmaki ofishin ƴan sanda, inda suka harbe jami’ai biyu da ke bakin aiki a nan take.

Al’amarin ya auku ne a daren Juma’a wayewar Asabar, wanda ya jefa jama’a cikin firgici tare da sanya su gudu domin neman tsira a lokacin da ƴan ta’addan suka yi ta harbe-harbe.

A cewarsa shaidun gani da ido, maharan sun kutsa cikin ofishin ƴan sandan ne wanda ke kusa da Otal ɗin Kamyim a Kurmin-Bi Zonkwa, sannan suka buɗe wa jami’an wuta.

Majiyoyi sun shaida wa manema labarai cewa ta yiwu ƴan bindigan sun kai harin ne da nufin kuɓutar da wasu ɓata-gari da aka kama a garin Kachia da ke Ƙaramar Hukumar Kachia a jihar.

Daga bisani sun gano cewa ba a nan aka tsare mutanen nasu ba, inda suka tsere bayan halaka jami’an biyu bisa amfani da tsegumin ƙarya.

Tuni mutanen da suka tsere suka koma yankinsu bayan an baza ƙarin wasu jami’ai wajen da nufin dawo da zaman lafiya.

By Babaji