
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Neja Hon. Abdulmalik Mohammed Sarkin-Daji ya jinjina wa rundunar sojojin Nijeriya bisa nasarar atisayen ceto mutane 70 da aka yi garkuwa da su a sassan jihar.
Haka kuma, ya baya wa Hukumar Tsaro ta Farin ƙaya (DSS) da wasu hukumomin tsaro akan ayyukan haɗin-gwiwa mai ƙarfi da taimakon da suka bayar da ya kai ga samun nasarar atisayen, wanda aka ƙaddamar a Ƙaramar Hukumar Mariga da wasu yankunan mazaɓar Neja ta Arewa.
Hon. Sarkin-Daji ya bayyana haka ne a wata sanrwa daga Shugabar sashen hulɗa da jama’a na majalisar, Mairo Adamu Mani, ranar Lahadi.
Ya bayyana atisyarna matsayin numfasawa ga ƙauyukan da abin ya shafa, yana mai cewa ƙwarewar dakarun sojojin da sauran hukumomin tsaro ya yi silar halaka ‘yan bindiga da dama da kama wasu daga cikinsu, sannan kuma aka ceto waɗanda aka yi garkuwa da su cikin aminci.
A cewarsa, ceto mutane 70 ɗin ya nuna ƙarara cewa sojojin da sauran jami’an tsaro sun sabunta ƙoƙarinsu wajen ganin sun kawo ƙarshen ayyukan garkuwa da sauran laifukan ta’addanci a jihar.
Kazalika, ya tabbatar wa jami’an tsaron cigaba da bada goyon baya daga ɓangaren gwamnatin jihar, yana jaddada aniyarta ta ƙarfafa wa ƙoƙarin fannin tsaro a sassan jihar.
