Kalaman John Kerry sun nuna girman kai na ƙasashen Yamma

Spread the love

Daga BELLO WANG

Kalaman da manzon musamman na shugaban ƙasar Amurka mai kula da aikin tinkarar sauyawar yanayi John Kerry ya furta, a taron ministocin ƙasashen Afirka kan aikin kare muhalli, wanda ya gudana a ƙasar Senegal a kwanan baya, sun ba ni mamaki sosai.

Saboda a gaban wakilan dukkan ƙasashen Afirka, mista Kerry ya ce ƙasashe masu sukuni, ba su da wani nauyi na tarihi game da batun sauyawar yanayin duniya.

A ganinsa, aikace-aikace na ɗaukacin dan Adam ne ke sa ake samun matsalar dumamar yanayi, saboda haka, ko da wata ƙasa dake fama da koma bayan tattalin arziki a nahiyar Afirka, wadda ke jin raɗaɗin bala’i daga Indallahi da sauyawar yanayin duniya ta haddasa, ya kamata ta ɗauki nauyi na tinkarar matsalar sauyawar yanayin da kan ta.

Kana ƙasashe masu sukuni ba sa buƙatar biyan diyya ga ƙasashen masu tasowa.

To amma mene ne gaskiyar wannan batu?

Sanin kowa ne, sannu a hankali, aikace-aikacen dan Adam na yin tasiri kan muhallin duiya.

Tun kafin ƙasashe masu tasowa su fara raya masana’antunsu, ƙasashen yamma masu sukuni sun riga sun kwashe shekaru fiye da 200, suna ƙoƙarin bunƙasa ɓangaren masana’antu, tare da fitar da ɗimbin iska mai ɗumama yanayi, da gurbata muhallin duniya sosai.

Hakan ya sa dukkan ƙasashe masu tasowa ke ɗauke da ra’ayin cewa, kamata ya yi, ƙasashe masu sukuni, da ƙasashe masu tasowa su ɗauki nauyi na bai daya, amma masu bambanci da juna, a yayin da ake tinkarar batun sauyawar yanayi.

Wannan ra’ayi ya nuna adalci, da dacewa da al’adar mutanen duniya, ta sanya wanda ya gurbata muhalli biyan diyya.

Sai dai maganar Kerry ta saɓa wa wannan ra’ayi na bai ɗaya na ɗaukacin ƙasashe masu tasowa.

Lamarin da ya sanya ‘yan Afirka fushi sosai: Wasu ƙungiyoyin jama’a da yawa na ƙasashe fiye da 40 dake nahiyar Afirka, sun nuna takaicinsu, inda suka ce John Kerry ya yi wasan fatar baki ne kawai, kana ya halarci taron ne don neman janyo hankalin mutanen duniya kan hulɗar dake tsakanin Amurka da ƙasashen Afirka.

Haƙiƙa, zancen Kerry ya nuna yadda ƙasar Amurka, da sauran ƙasashen yamma suke da girman kai.

A ganinsu, yadda ƙasashe masu tasowa suke tsayawa kan samun adalci, wani yunƙuri ne na neman kudi kawai.

Ban da wannan kuma, Kerry ya yi gargaɗi ga ƙasashen Afirka, cewa kar su zuba kuɗi da yawa a aikin haƙar iskar gas, duk da cewa akwai ƙasashen Afirka da yawa da suke ƙoƙarin raya ɓangaren iskar gas, don tabbatar da tsaron makamashi.

A cewar John Kerry, ya kamata a raya makamashi da ake sabuntawa, maimakon iskar gas. Ya ce, “kar ku maimaita kurakuran da muka yi a baya.”

Nufinsa shi ne, saboda ƙasashen yamma sun taba yin kurakurai, don haka a yanzu sun fi sanin hanya mai dacewa da ya kamata a bi ta.

Ya kamata ƙasashen Afirka da sauran ƙasashe masu tasowa su bi umarnin ƙasashen yamma.

A nan an nuna girman kai matuka.
Ta hanyar sauraron maganar John Kerry, za mu gane cewa, aikin tinkarar sauyawar yanayi ba shi da sauki.

Kuma ba za a cimma nasara ba, sai dai in ƙasashen Yamma daina nuna girman kai da son kai, sa’an nan su yi cuɗanya da kasashe masu tasowa cikin daidaito.

By Editor