Shugaba Xi ya aike da wasiƙar taya murnar buɗe taron dandalin ƙasa da ƙasa a fannin samar da kayayyakin masana’antu

Spread the love

Daga CMG HAUSA

Shugaban ƙasar Sin Xi Jinping, ya aike da wasiƙar taya murnar bude taron dandalin ƙasa da ƙasa a fannin tabbatar da juriya da ɗorewar tsarin samar da hajojin masana’antu da ake shigarwa kasuwanni.

Xi Jinping ya aike da wasiƙar ne a Litinin din nan, ga mahalarta taron dandalin da aka buɗe a birnin Hangzhou, fadar mulkin lardin Zhejiang na ƙasar Sin.

Cikin wasiƙar tasa, shugaba Xi ya ce wanzar da juriya da daidaito a fannin samar da hajojin masana’antu da ake shigarwa kasuwanni, hanya ce ta tabbatar da ingiza ci gaban tattalin arzikin duniya, tare da biyan buƙatun bai ɗaya na al’ummar duniya baki ɗaya.

Xi ya ƙara da cewa, Sin a shirye take ta tabbatar da tsarin samar da hajojin masana’antu da ake shigarwa kasuwanni, ya zamo mallakin al’ummun duniya baki ɗaya, kuma za ta kare tsaro da daidaiton tsarin, kana za ta aiwatar da ƙwararan matakai na zurfafa haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa, a fannin samar da hajojin masana’antu da ake shigarwa kasuwanni, tare da tabbatar da cewa, dukkanin ƙasashen duniya sun ci gajiyar wannan ci gaba.

Mai fassara: Saminu Alhassan

By Editor