Osinbajo ya isa London don halartar jana’izar Sarauniya Elizabeth ll

Daga BASHIR ISAH

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya isa birnin London a ranar Lahadi domin halartar jana’izar Sarauniya Elizabeth ll.

A ranar Asabar Osinbajo ya bar Abuja zuwa Birtaniya inda zai wakilci Nijeriya wajen wasu muhimman ayyuka, ciki har da jana’izar Marigayiya Sarauniya Elizabeth.

Hadimin Osinbajo kan harkokin yaɗa labarai, Laolu Akande, ya ce bayan da mataimakin Shugaban Ƙasar ya isa London a ranar Lahadin, ya ziyarci inda aka ajiye gawar marigayiyar a Westminster.

Kazalika, ya ce, Osinbajo ya sanya hannu a littafin da mahalarta jana’izar kan rubuta sunayensu. Kana ya ce, “Nijeriya ta shiga sahun ƙasashe renon Ingila da sauran ƙasashen duniya wajen miƙa ta’aziya ga ahalin marigayiyar.”

Daga bisani, Sakataren Harkokin Waje da Diflomasiyya na Birtaniya, James Cleverly, ya tarbi Farfesa Osinbajon kamar yadda hadiminsa Akande ya bayyana a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Tiwita.

Da yammacin Lahadi ake sa ran Sarki Charles III da Sarauniya Consort Camilla za su karbi baƙuncin manyan baƙin da suka halarci birnin don jana’izar a fadar Buckingham.