Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe
Ɗan takarar jam’iyyar APC a zaɓen cike gurbin kujerar majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar Gombe/Kwami/Funakaye, Dakta Usman Maijama’a Kallamu, ya roƙi al’ummar mazaɓar da su mara wa jam’iyyar baya a zaɓen da za a gudanar ranar 19 ga Satumba, 2026.
Kallamu ya yi wannan kiran ne yayin da yake zantawa da manema labarai a lokacin yaƙin neman zaɓensa gabanin zaɓen da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) za ta gudanar.
Ya buƙaci masu kada ƙuri’a da suka cancanta a ƙananan hukumomin Gombe, Kwami da Funakaye da su fito da yawa domin sauke nauyin da ke kansu na ƙasa, tare da kaɗa ƙuri’u ga APC.
Ɗan takarar ya ce ya yanke shawarar shiga takarar ne saboda burinsa na samar da ingantaccen wakilci da kuma bayar da gudunmawa wajen bunƙasa tattalin arziki da rayuwar al’ummar mazaɓar.
Kallamu ya kuma yi kira ga magoya bayansa da sauran masu ruwa da tsaki da su tabbatar da zaman lafiya kafin zaɓe, lokacin gudanar da shi da kuma bayan kammalawa.
Ya buƙaci jama’a da su guji tashin hankali, tsokana da duk wani abu da zai iya kawo cikas ga gudanar da zaɓen cikin lumana.
Dan takarar ya bayyana kwarin gwiwarsa kan samun goyon bayan masu kada ƙuri’a, inda ya tabbatar wa al’umma cewa idan aka zaɓe shi, zai bai wa muradun jama’a da jin daɗin rayuwarsu muhimmanci.
Saboda haka, ya roƙi masu kaɗa ƙuri’a da su ba shi damar wakiltarsu ta hanyar kaɗa ƙuri’a ga APC a ranar 19 ga Satumba.
INEC ta sanya ranar 19 ga Satumba, 2026, domin gudanar da zaɓen cike gurbin kujerar Majalisar Wakilai ta tarayya mai wakiltar mazaɓar Gombe/Kwami/Funakaye.
