
Daga BELLO A. BABAJI
Matatar Man fetur ta kamfanin Ɗangote, ta sanar da rage farashin litar fetur zuwa N899.5.
Jami’in Labaran kamfanin, Anthony Chiejina ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a safiyar ranar Alhamis.
Ya ce hakan na zuwa ne a lokacin da al’ummar Nijeriya ke shirin gudanar da bukukuwan ƙarshen shekara don sauƙaƙe musu tsardar rayuwa da ake fama da ita a ƙasar.
A watan Nuwamba ne kamfanin ya rage farashin zuwa N970 inda a yanzu kuma dawo da shi N899.50.
Ya kuma sanar da cewa kamfanin ya bada dama ta musamman ga kwastomominsa na sayen dai-dai adadin da aka saya kuɗi a hannu a hali na bashi.
Ya ce hakan wani mataki ne da kamfanin ya ɗauka na rage farashin sufurin ababen hawa, ya na mai godiya ga al’umma kan irin goyon bayan da suke ba su.
