
Daga BELLO A. BABAJI
A yau ne Antoni-Janar na Ƙasa kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi zai tattauna da Majalisar Dattawa kan batun kuɗirin gyaran haraji da Shugaba Bola Tinubu ya gabatar wa majalisa.
Bayan cecekuce da aka samu ne game da ƙudirin kan wasu saɗarori da al’umma ke ganin ka iya haifar da matsaloli ga harkokisu na yau da kullum, sai Shugaba Tinubu ya umarci Antonin da ya gana da majalisa don samun maslaha game da batun.
A gefe guda kuma, Majalisar ta shirya wani kwamiti dazai gana da ministan shari’ar.
Shugaban kwamitin, Sanata Abba Moro ya bayyana wa manema labarai cewa an gayyaci Ministan ne tare da Shugaban Hukumar Tattara kuɗaɗen shiga ta Ƙasa, Zacch Adedeji.
Makonni biyu da suka gabata ne Majalisar ta samar da kwamitin don warware matsalolin da ke tattare da wasu wurare acikin takardar ƙudirin.
