
Daga BELLO A. BABAJI
Jami’an tsaron ƴan sandan farin kaya (DSS), sun yi ram da shugaban Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS), Semiu Adeyemi Adeniran a ofishinsa na hukumar.
Jaridar News Point Nigeria ta ruwaito cewa, an kama shugaban hukumar ne kan alaƙa da batun sata da wani rahoton tsaro da hukumar ta fitar a ranar Talata.
A baya ne NBS ta fitar da rahoton cewa ƴan Nijeriya sun biya kuɗin fansa da adadinsa ya kai Naira tiriliyan 2.23 daga watan Mayun 2023 zuwa Afrilun 2024.
Rahoton ya bayyana cewa waɗannan kuɗaɗe ne da magidanta suka biya sakamakon ayyukan garkuwa da mutane da ya shafe su wanda hakan ke nuna yadda ta’addanci ke cigaba da ta’azzara a Nijeriya.
Rahoton ya ƙara da cewa, aƙalla adadin ayyukan sata ya kai miliyan 51.89 a faɗin Nijeriya na tsawon wannan lokacin.
Wani jami’in NBS da ya buƙaci a sakaye sunansa, ya ce DSS ta kama Mista Adeniran ne a ofishinsa ƙasa da sa’o’i 24 bayan fitar da rahoton.
Sa’o’i kaɗan da suka gabata ne NBS ta fitar da sanarwar cewa an samu wasu madatsan na’ura sun datse adireshinta na yanar gizo.
