Al’ummar Bichi na buƙatar a gina masu jami’a

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Ƙungiyar Cigaban Matasan Bichi wato Bichi youth development Forum ƙarƙashin gamayyar ƙungiyoyin matasa da cigaban ƙaramar hukumar Bichi, sun buƙaci gwamnatin Kano da ta samar masu da jami’a domin cigaban ilimi a wannan yanki,

Ƙungiyar ta yi wannan Kiran ne yayin taron jin ra’ayin jama’a da aka gudanar a majalisar dokokin jihar Kano akan kasafin kuɗi na 2024/2025, wanda gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya miƙa wa majalisa.

Gazali Abubakar Isah Bichi (Gaza) wanda shi ne ya wakilci al’ummar ta Bichi ya bayyana yankin a matsayin matattara ta ilimi, inda ya ce

“Babban giɓin da muke da shi a wannan yanki na mu shi ne na rashin jami’a, domin za kaga kowane yanki da muke da shi guda uku a jihar Kano, duk suna da jamia ta gwamnatin tarayya ko ta jiha ko mai zaman kanta, amma yankinmu an barshi a baya.

“A baya akwai tsohon ƙudiri na gina jami’ar harkar lafiya da kimiyya, wanda yanzu haka akwai fili mallakin gwamnatin Kano, wannan ne yasa muke jaddada roƙon mu akan majalisa ta sake gabatar da wannan ƙudirin domin a tabbatar an shigar da wannan ƙudirin cikin kasafin kuɗin 2024/2025 don a yi wannan jami’a da za ta amfani al’ummar wannan yanki na mu na ƙaramar hukumar Bichi” inji Garzali

Da ya ke mayar da jawabi shugaban kwamitin kasafin kuɗin na majalisar, Alhaji Aminu Sa’adu Ungoggo, ya tabbatar da cewa majalisar ta duƙufa wajen zartar da ƙudirorin ‘yan ƙasa.

Sannan ya yi nuni da cewa za su yi nazari sosai kan buƙatun al’umma da shigar da muradan jama’a.

Blueprint Manhaja ta ruwaito cewa taron ra’ayoyin jamaar ya samu halartar ƙungiyoyin farar hula, ƙungiyoyin al’ummar da na sakai baki ɗaya.

By ukarofi