Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
Manajan daraktan tuntuɓa ta Jami’ar Khalifa Isyaka Rabiu dake Kano, wato Khairun Consultancy Limited, Dokta Naja’atu Bala Rabiu ta ce an buɗe kamfanin ne domin saye da sayarwa da ƙirƙirar abinda babu, ko saye da sayarwar kaya ga jami’ar kamar yadda suke a halin yanzu, amma nan gaba za su iya faɗaɗa shi zuwa wajenta a matsayin kamfani.
Ta bayyana haka ne da take ƙarin haske ga ‘yan jarida, ta ce sannan kuma suna yin ƙananan kwasa-kwasai da bita da bayar da horo ga ‘yan kasuwa da ɗalibai da ƙungiyoyin masu sana’o’i da sauran mutane ya danganta da buƙatarsu, ko da ba sa yin irin horon da ake nema za su iya haɗin kai da wanda ke son ayi horon su haɗu a ɗauki nauyin a gayyato masana a duk inda suke a gudanar a jami’ar in an kammala za a bada shaidar ka zo ka yi horo ko bita a jami’ar.
Ta ƙara da cewa suna kuma da niyyar shirya kwasa-kwasai na taƙaitaccen lokaci na bayar da shaidar difiloma cikin wata shida ko wata uku nan gaba wanda shaidar difilomar zai bada damar samun shiga jami’a, amma yanzu suna jiran samun sahalewa ne kafin su soma, abinda suke yanzu shine bada shaidar satifiket ba su soma na difiloma ba.
Dakta Naja’atu ta ce hatta gwamnati suna so su sami dangantaka da za su riƙa ɗaukar nauyin bada horo ga ma’aikata a fannoni daban daban na Gwamnatin jiha da na ƙananan. Hukumomi kuma za su fifita ba da horon ne da harshen Hausa, amma a bada shaida ta jami’ar akan duk horo da aka gudanar a jami’ar ta ƙarƙashin ofishin na tuntuɓa.
Dakta Naja’atu Bala Rabiu ta ce wannan tsarin tuntuɓa na jami’ar da yake kamfani ne mai zaman kan shi a ƙarƙashin jami’a yake, ba shi da damar yin digiri, a ƙarƙashin su duk wani abu da zai samarwa da jami’ar kuɗi sune da alhakin samarwa banda wanda take samarwa daga ɗalibai, amma na yau da kullum zai zama a ƙarƙashin su, hanyoyi shigowar kuɗi a jami’ar daga saye da sayarwa da yin duk wani abu da zai samar da kuɗaɗe duk akansu yake .
Ta bayyana cewa ba su bambanta da sauran jam’i’o’i da yawa da suka daɗe ba, saboda sun samu wani jagoranci daga wasu jami’o’i sun je wajen su sun yi magana da su sun ba su shawarwari sai suka zo suna kwaikwayon su da kuma ƙara tasu basirar akai.
Dakta Naja’atu Bala Rabiu ta yaba irin ƙoƙarin mataimakin shugaban jami’ar na Khairun, Farfesa Abdulrashid Garba ta ce shine asali ya goya musu baya wajen ƙirƙirar sashen tuntuɓar da ƙaddamar da shi ya riƙa hoɓɓasa akai wajen samar da cibiya, domin yin abubuwa na kasuwanci da za su samar da kuɗi dan ragewa masu jami’ar nauyi da yake kansu.
Ta ce duk kuɗi da ake samu yanzu daga ɗalibai ne, kuma abinda ake musu baya wuce a kashi 100 ya yi musu 10 duk abinda suke na yau da gobe a hannun masu makaranta yake fitowa, sai ya ce su fito da sabon tsari da zai zama ana iya samar da wani kuɗin banda wannan ta ina ? ya ga jami’o’i suna yi tunda shi daga Jami’ar Bayero yake har ya yi mataimakin, mataimakin, shugaban jami’ar da kuma riƙon mataimakin shugaban jami’ar ta Bayero, saboda haka yake ganin su kwaikwayi jami’oi da suka daɗe, suma su fito da wani tsari na shigowar kuɗi don tallafawa gudanar da makarantar.
Dakta Naja’atu Bala Rabiu ta ce su yanzu suka fara, basu soma samun komai ba daga tsare-tsaren su, suna fatan nan gaba burinsu zai cika za su samu abinda za su riƙa tallafawa su ragewa masu jami’ar nauyi.
