Kamfanin Netflix zai bar Nijeriya

Shahararren kamfanin samar da fina-finai na intanet, Netflix, ya sanar da ficewarsa daga kasuwar Najeriya bayan shekaru shida, sakamakon tsananin taɓarɓarewar tattalin arzikin ƙasar ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Rahotanni daga Peoples Gazette sun bayyana cewa rashin ƙwarin gwiwa da kamfanin ke samu daga masu biyan kuɗi da kuma matsin lambar darajar naira ya sa dole su yanke wannan shawara.

Wani jami’i daga Netflix wanda ya zanta da Peoples Gazette cikin sirri ya bayyana cewa, “Mun rasa yawancin masu biyan kuɗi, kuma sauyin darajar naira da dala ya ƙara mana matsaloli.” Wannan mataki ya biyo bayan ƙarin hauhawar farashi da Ofishin Ƙididdiga na Ƙasa (NBS) ya wallafa a baya-bayan nan, wanda ke nuna halin ƙuncin tattalin arziki da Nijeriya ke ciki.

Netflix ya fara ayyukansa a Nijeriya a shekarar 2018, inda ya samar da fim ɗin Lionheart na Nollywood wanda aka yi marhabin da shi sosai saboda ingancin sa da yadda ya nuna fasahar Nijeriya ga duniya. Wannan mataki ya haifar da dama ga masana’antar fina-finai ta ƙasar don isar da ayyukansu zuwa ga masu sauraro na duniya.

Sai dai, duk da cewa kamfanin ya fuskanci ƙalubale a wasu kasuwanni, Najeriya ce ta zama kasa ta farko daga cikin manyan kasuwanni da Netflix zai rufe ayyukansa baki ɗaya. Wannan ficewa ya zo ne da alhini ga masana’antar Nollywood da masu sha’awar kallon fina-finai ta intanet a ƙasar.