Kamfanonin Ƙasar Sin sun gina layin dogo da ya haura tsawon kilomita 10,000 a sassan nahiyar Afirka

Daga CMG HAUSA

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Zhao Lijian, ya ce ƙarƙashin dandalin bunkasa hadin gwiwar Sin da nahiyar Afirka, kamfanonin ƙasar Sin sun gina layin dogo da tsayin sa ya zarce kilomita 10,000, da kusan kilomita 100,000 na titunan mota, da kusan gadoji 1000, da kusan tashoshin ruwa 100, da tarin asibitoci da makarantu a sassan nahiyar Afirka.

Zhao Lijian ya bayyana hakan ne, yayin taron manema labarai na yau Talata, lokacin da yake amsa tambayar da aka yi masa dangane da sabuwar gadar Wami da aka bude a baya bayan nan a ƙasar Tanzania, wadda wani kamfanin ƙasar Sin ya gina.

Zhao ya ƙara da cewa, har kullum ƙarancin manyan ababen more rayuwa na zamewa ƙasashen Afirka “Kadangaren bakin tulu” ta fuskar ci gaba.

Daga nan sai ya jaddada aniyar ƙasar Sin, na ci gaba da rike gaskiya da amana, da kare haƙiƙanin yanayi na adalci da cimma moriyar juna, tare da aiwatar da matakan bunƙasa haɗin gwiwa da ƙasashen Afirka a fannoni daban daban.

Kazalika Sin za ta dage waje kare moriyar ta da ta al’ummun Afirka, kana za ta shigar da sabon kuzari wajen gina al’ummar duniya mai makomar bai ɗaya tsakanin ta da kasashen Afirka a wannan sabon zamani.

Ai fassara: Saminu Alhassan