Tarihin Sarakunan Fulani na Kano (IV)

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

A makon jiya muka cigaba da kawo wa masu karatu taƙaitaccen tarihin sarakunan Fulani waɗanda suka fara mulkin ƙasar Kano tun daga jihadin Shehu Usman Ɗan Fodiyo kawo yau. To yau za mu cigaba faga inda muka tsaya.

Muhammadu Sanusi I (1953 zuwa 1963) Miladiyya:

Sarki Muhammadu Sanusi shi ne Sarki na 53 a jerin Sarakunan Kano, sannan Sarki na 11 a jerin Sarakunan Fulani.

Sarki Muhammadu Sanusi babban malamin addini ne kuma sufi. Mutum ne marar tsoro, managarci, sannan masanin addini. Da hawansa karagar mulkin Kano ya fara da tsarkake Masarautar Kano daga ƙazantar giya da sata da kuma karuwanci.

Sarki Muhammadu Sanusi shi ne Sarkin da ya riqa zartar wa mashaya giya haddi a sarari, karuwai kuma yana tsare su a gidan kaso, su je su yi idda bayan gama iddarsu sai kuma su yi aure; idan sun samu miji. Samun wannan miji shi ne belin karuwa.

A zamanin Sarki Muhammadu Sanusi an ƙara gina wasu makarantu da asibitoci da dai sauran kayan more rayuwa. A lokacinsa aka gina Makarantar Babbar Firamare ta Birnin Kudu a 1954, sannan a zamaninsa aka giggina makarantun U.P.E. a wasu unguwannin Kano uku da suka haɗa da Jarƙasa da Makafin Dala da kuma Kurawa a 1960.

Sannan a zamaninsa aka gina Makarantar Horar da Malamai (Kano Teachers College) a 1957. Sannan a zamaninsa aka gina katafaren Asibitn Kashi na Dala. Da sauran muhimman ayyuka da aka gudanar a zamaninsa.

Muhammadu Inuwa Abbas (1963):

Sarki Muhammadu Inuwa shi ne Sarki na 54 a jerin Sarakunan Kano, sannan Sarki na 12 a jerin Sarakunan Fulani. An yi masa sarautar Kano lokacin yana riƙe da muƙamin Turakin Kano. Sannan ya yi hakimi a Bichi, da kuma Gundumar Minjibiri wacce ta haɗa da Kunya da Kuru kafin zamowarsa Sarki.

Sarki Muhammadu Inuwa Abbas bai yi tsawon zamani a kan karagar mulkin Kano ba. Ya yi sarauta ta tsawon wata shida kacal. Ya rasu a 1963. Allah Ya jiƙansa, amin.

Sarkin Kano Ado dan Abdullahi Bayero (1963 Zuwa 2014):

Alhaji Ado Bayero. Shi ne Sarki na 55 a jerin Sarakunan Kano kuma Sarki na 13 a Sarakunan Fulani. Tun daga farkon sarautar Kano zuwa yau (2017), marigayi Alhaji (Dokta) Ado Bayero shi ne Sarkin da ya fi kowane Sarki daɗewa a kan karagar mulkin Kano. Sarkin ya mulki Kano na tsawon shekaru 51 tun daga 1963 har zuwa 2014.

Tsohon ma’aikacin banki, Wakilin Doka, ma’aikacin Hukumar En’e (NA), kuma tsohon Wakilin Nijeriya a ƙasar Senegal. An samu daraja da martabar Masarautar Kano ta ɗaukaka a iya tsawon mulkinsa.

An haifi Alhaji Ado Bayero a ranar 25 ga Yunin 1930 (Wikipedia, 2014; Mahmood, 2014; Umar, 2008). Shi ɗan Sarki Abdullahi Bayero ɗan Sarki Muhammadu Abbas ɗan Sarki Malam Ibrahim Dabo, Bafullatani kuma Basulluɓe. Sunan mahaifiyarsa Hajiya Hasiya.

Tasowarsa:

Marigayi Alhaji Ado Abdullahi Bayero, ya fara karatunsa na addini tun yana ƙarami kamar yadda aka saba. Sannan daga baya aka saka shi a makarantar Midil ta Kano, kuma ya samu nasarar zarcewa zuwa Makarantar Koyon Larabci ta Kano (SAS) inda ya kammala a 1947. Ya kuma halarci Kwalejin Horar da Akawu-Akawu ta Zariya wadda ta zama Sashin Mulkin na Jami’ar Ahmadu Belleo da ke Zariya a 1952.

Ayyukan da ya yi:

Kafin zamowarsa Sarki, Ado Bayero ya yi aikin banki da The Bank of British West Africa har zuwa 1949, inda daga nan ya zarce Hukumar En’e (Natibe Authority) a matsayin Akawun Majalisa. A 1954 kuma aka zave shi a matsayin dan Majalisar Jihar Arewa da ke Kaduna. Daga kan wannan muqamin kuma aka yi masa Wakilin Doka na Kano tun daga 1957 zuwa 1962. Sannan ya zama Wakilin Nijeriya a Ƙasar Sanagal muƙamin da yana kansa aka yi masa Sarautar Kano.

Zamowarsa Sarki:

Alhaji Ado Abdullahi Bayero, ya zamo Sarkin Kano ne a 1963. Shi ne sarkin Kano na 55, sannan Sarki na 13 a jerin Sarakunan Fulani.

Gudunmawar da ya bayar:

Alhaji Ado Bayero ya bayar da gagarumar gudunmawa da ba zai yiwu a ƙididdige ta ba. Shi ne Sarkin da Kano ta zama jiha a hannunsa. Ya yi zamani da gwamnoni 15 kuma ya yi aiki da shugabannin ƙasa 13. Ya ga canje-canje iri-iri. Da bakinsa ya ke cewa, “Da mu muke yi, aka zo ana yi da mu, yanzu kuma sai an yi a gaya mana.” (Mahmood, 2014).

Sarki Ado Bayero ya ciyar da Kano gaba, kama daga taimakon ɗaiɗaikun mutane; dalilin da ya sa ake yi masa kirari da ‘Baya goya marayu, Uban marasa uba,’ har zuwa kan ƙungiyoyi da gina masallatai da makarantu da sauran ayyukan alheri masu dambin yawa. Bari mu leqa Umaru (2008), mu ɗan tsakuro:

  1. Kira zuwa ga addinin Musulunci da tsayar da ibada da musuluntar da waɗanda ba Musulmi ba.
  2. Gina masallatai da makarantun Islamiyya a cikin birni da ƙauyukan Kano.
  3. Nuna soyayya ga malamai da masu wa’azi da sauran masu yi wa addini hidima.
  4. Bada goyon baya ga aiwatar da shari’ar Musulunci da koarfafa aiki da ita da zartar da hukunce-hukunce bisa tafarkinta daidaitacce.
  5. Sake gina katangar gidan Sarki da duwatsu da siminti.
  6. Lulluɓe titunan cikin gidan Sarki da tayil mai kyau.
  7. Sake gina gidajen Wambai da Galadima da Waziri da gidajen hakimai da ke ƙananan hukumomi.
  8. Wadata hakimai da ababen hawa.

Rasuwarsa:

Alhaji Ado Bayero ya mulki Kano na tsawon shekara 51. Ya rasu a ranar 6 ga Yunin shekarar 2014. Ya rasu ya bar ’ya’ya maza 31 da ’ya’ya mata 30. Allah Ya jiƙansa da rahama, amin.