KANNYWOOD: Abba Almustapha ya fara kama ’yan Kwankwasiyya

Spread the love

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja

Shugaban Hukumar Tace Finafinai na Jihar Kano, Abba Almustapha, ya yi wani wawan kamu a jihar, inda ya kama ɗaya daga cikin zaratan siyasar Kwankwasiyya a masana’antar shirya finafinai ta Kannywood mai suna Umar UK.

An kafa wannan tarihi ga siyasar Kwankwasiyya ne a jiya Laraba, 2 ga Yuli, 2025, bisa zargin da hukumar ta ke yi wa UK na fitar da shiri mai dogon zango mai suna Garwashi ba bisa ƙa’ida ba, wanda suka ɗauki nauyi tare da Mai Taimaka Wa Gwamna ta Musamman, Fauziyya D. Sulaiman.

Jami’an Hukumar Sibil Difens ne suka yi dirar mikiya a ofishin Umar UK da ke yankin Hotoro a harabar CTV cikin birnin Kano yayin da suka isa da gefen maraice, inda suka yi awon gaba da shi da manajan kamfanin, Mubarak Abba, zuwa ofishinsu da ke rukunin gidaje na Kwankwasiyya a kan titin Zaria Road.

Umar UK dai yana ɗaya daga cikin furodusoshi masu shirya finafinai masu nagarta, wanda shirin Garwashi na ɗaya daga ciki, to amma Hukumar Tace Finafinai ta Kano a ƙarƙashin jagorancin Abba Almustapha ba ta yi ƙasa a gwiwa wajen kama shi ba.

Wannan ne ya sanya da yawa ke kallon lamarin a matsayin siyasar cikin gida ce ta janyo rikicin.wata majiya a tafiyar Kwankwasiyya ta shaida wa Bluerint Manhaja cewa, “ba a daɗe da bai wa Abba Almustapha muƙamin shugabancin Hukumar Tace Finafinai ba aka fara samun takun saƙa tsakaninsa da yawancin Kwankwasawa na Kannywood.

“Ya fara rikici ne da Sunusi Oscar, yanzu kuma da Umar UK ya ke yi, domin ba shi kaɗai ne bai yi rijistar shirin na dogon zango a hukumar ba. Kuma me ya sa bai saka a kama Fauziyya ba tunda tare suka ɗauki nauyin fim ɗin”

Yanzu dai bayan jin ba’asin yadda lamarin tuni hukumar Sibil Difens ta bayar da belin Umar UK da Mubarak Abba, inda za a ƙara zama washegari Alhamis da safe.

A yanzu haka dai lamarin ya janyo abin magana a ciki da wajen masana’antar, inda ake har ta faman yi wa ’yan Kwankwasiyya da gwamnatinsu shaguɓe.

By ukarofi