Kotun Amurka ta hana Diddy beli bayan samun sa da laifi

Spread the love

Daga AISHA ASAS

Kotun Tarayya ta birnin New York ta kaca ƙwarya a kan hamshakin attajiri kuma fitaccen mawakin nan, Sean “Diddy” Combs, inda ta ƙi amincewa da buƙatarsa ta beli bayan samun sa da laifin safarar mata domin ayyukan lalata.

Alƙali Arun Subramanian, wanda ya jagoranci shari’ar, ya bayyana cewa, ba zai saki Combs ba kasancewar yana da dabi’a mai matuƙar tayar da hankali da ƙyamar aikata doka, kamar yadda aka gabatar a cikin shari’ar.

“An bayyana a fili cewa yana da halayen da ke barazana ga al’umma. Hatta lauyoyinsa sun amince da wasu daga cikin waɗannan laifuka,” inji alƙalin.

Ko da yake an wanke Combs daga manyan laifuka na cin zarafin jima’i da ƙungiyar laifi (racketeering), ta samu da laifi a kan tuhuma biyu na safarar mata domin karuwanci, wanda kowanne na ɗauke da hukuncin shekaru 10 a kurkuku. Za a sake zama ranar Talata mai zuwa domin a tsara ranar hukunci.

Bayan hukuncin, an bayyana yadda Combs ya kalli iyalinsa da hawaye, yana cewa: “Ina ƙaunarku… Ku kasance masu ƙarfi. Zan gan ku idan na fito.”

Kafin ya aika masu da sumbata ta iska, sannan jami’ai suka fice da shi daga kotu.

Lauyansa, Marc Agnifilo, ya bayyana hukuncin a matsayin “nasara ga tsarin shari’a”, yana mai cewa: “Mun ci nasara a kan tuhumar cin zarafi da ƙungiyar laifi ke masa, wannan babban abu ne.”

Ita ma lauya Teny Geragos ta ce: “Mun jima muna cewa Sean Combs bai taɓa cin zarafin jima’i ba, yau an tabbatar da hakan.”

Cassie Ventura, ɗaya daga cikin waɗanda suka bayar da shaida, ta aike da wasiƙa zuwa ga alkali, inda ta ce: “Combs yana iya zama barazana ga lafiyar mu.”

Lauyan wata shaidar shari’ar, Dawn Richard, ta bayyana fushinta da hukuncin, tana mai cewa: “Za mu ci gaba da neman adalci ta hanyoyin shari’ar farar hula.”

Wajen kotun ya rikiɗe tamkar sansanin shaƙatawa ko zanga-zanga. Wasu na ihu suna murna, wasu kuma na cewa an ci su da tuwo. Rundunar ‘yan sanda ta kasa ta tashi haikan don hana rikici.

Kodayake an shirya zaman hukunci ranar 3 ga Oktoba, 2025, alkali ya nuna cewa za a iya rage lokacin idan masu kare Combs sun yarda da cire binciken da ake yi kafin yanke hukunci. Sai dai mai gabatar da kara, Maurene Comey, ta jaddada cewa:b“Combs mutum ne mai haɗari, mai taurin kai da jin daɗin aikata laifi. Bai nuna nadama ba ko sauyawa.”

Tarihin shari’ar Sean Combs ya zama ƙararrawa ga shahararru: Kuɗi ba zai share laifi ba, kuma duniya na kallon yadda adalci ke tafiya, komai tasiri ko ƙima. Kotu ta nuna cewa babu wani sama da doka.

By ukarofi