Daga AISHA ASAS
“Na san ina tsaye a wuri mai tsarki lokacin da na fara aiki da ita.”
Fitaccen ɗan wasan fina-finai kuma mai gabatar da shirin faifai (podcast), Tobi Makinde, ya bayyana irin gagarumar rawar da shahararriyar mai shirya fina-finai kuma jaruma Funke Akindele ta taka wajen ɗaga darajarsa da ƙwarewarsa a harkar fim.
A wata hira da ya yi da jaridar Sunday Scoop, Makinde ya ce, aiki da Akindele a kan manyan fina-finai kamar ‘A Tribe Called Judah’ da ‘Everybody Loves Jenifa’ ya sauya masa akalar rayuwarsa gaba ɗaya.
“Lokacin da na fara aiki da Funke, na fahimci ina tsaye a wuri mai tsarki na ƙwarewa. Ba wai kawai tana da baiwa ba ce , tana da niyya, tsari da kuma azama ba kamar yadda muka saba gani ba,” inji shi.
Ya bayyana cewa, jagoranci da sadaukarwar Akindele wadda aka fi sani da Jenifa a wurin aiki sun kasance darussa masu zurfi da suka koyar da shi ba wai kawai fassara ba, har da yadda ake ɗaukar kai a matsayin ɗan ƙirƙira a harkar nishaɗi.
“Aiki da ita ya zamo darasi ne mai zurfi, ba kawai a fagen wasan kwaikwayo ba, har da yadda mutum zai gabatar da kansa a matsayin mai fasaha. Ya sauya yadda nake kallon komai a rayuwata.”
Tobi Makinde, wanda ya fara fitowa a fina-finai tun yana yaro, musamman a cikin fina-finai irin su ‘Kamsi’ da ‘Neighbours’, ya bayyana wata ganawa da wata masoyiyar aikinsa da ta ratsa zuciyarsa.
Ya ce, wata baiwar Allah ta zo da hawaye tana shaida masa cewa aikinsa ya taimaka mata wajen shawo kan wani mawuyacin lokaci a rayuwarta.
“Wannan ganawa ta sa na zurfafa tunani. Ta tuna min cewa aikin da muke yi ba ƙarami ba ne. Yakan shige duhun zuciya ya ɗauko haske,” inji shi.
Baya ga fitowa a fina-finai, Makinde ya shiga harkar faifai da shirin sa mai taken ‘The Tobi Makinde Show.’
Yayin da yake bayyana wannan sabuwar tafiya, ya ce, akwai bambanci mai yawa tsakanin rubutaccen fim da zantukan gaske na rayuwa kai tsaye a faifai.
“A fina-finai da talabijin, ana da rubutaccen shiri. Amma a cikin faifai, kai, baƙonka, da gaskiya kawai ke nan,” inji shi.
Wannan yabon ya ƙara ɗaga martabar Funke Akindele a idon jama’a, musamman ganin yadda aka fi saninta da tasiri mai kyau ga matasa masu tasowa a harkar fina-finai.
Tobi Makinde ya tabbatar da cewa, aikin da suka yi tare ya bar masa tarihi mai kyau, kuma zai ci gaba da amfani da darussan da ya koya daga gare ta a kowacce fuska ta rayuwa da ƙirƙira.
