Kano da Faransa sun ƙara dangantaka kan shirin gyaran sashen ruwa

Spread the love

Daga RABIU SANUSI a Kano

Gwamnatin Jihar Kano da Gwamnatin Faransa sun kara zurfafa hulɗarsu a ƙarƙashin Shirin Gyaran Sashen Ruwa na ƙasa, shirin da ke mai da hankali kan inganta walwalar jama’a, ƙarfafa tsarin gudanarwa da kuma tabbatar da ɗorewar samar da ruwan sha.

Wannan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamna, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Laraba.

A yayin tarbar tawagar jakadancin Faransa mai mutum takwas a Gidan Gwamnati, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tattauna da Jakadan Faransa a Nijeriya, Mista Marc Fonbaustier, kan ci gaban muhimman ayyukan ruwa da ake aiwatarwa a Kano tare da sabbin fannoni na haɗin kai.

Jakadan ya bayyana cewa girman tawagar da ya jagoranta na nuna irin muhimmancin da gwamnatin Faransa ke bai wa Kano da daukacin Arewacin Nijeriya. Ya ce Faransa da Nijeriya “suna da makoma daya,” inda manufarsa ita ce ganin an ƙara ƙarfafa hulɗar da ke tsakanin ƙasashen biyu, musamman a Jihar Kano.

Fonbaustier ya jaddada cewa shirin gyaran sashen ruwa na ƙasa ya fi karkata ga tasirin zamantakewa kamar inganta gudanarwa, horas da ma’aikata da tabbatar da ɗorewar samar da ruwa, maimakon mai da hankali kan kayan aiki kawai.

Ya tabbatar da cewa Faransa na ci gaba da tallafa manyan ayyukan sashen ruwa a Kano, tare da alƙawarin zurfafa hadin gwiwar nan gaba. “Hadin gwiwarmu da Kano ya ƙaru sosai, kuma tattaunawar da muka yi yau ta buɗe sabbin damammaki na faɗaɗa abota da aikin ci gaba,” inji shi.

Jakadan ya ƙara da cewa ɓangaren sufuri da inganta zirga-zirga na daga cikin sabbin wuraren haɗin kai da za a fara aiki a kansu nan gaba.

A nasa jawabin, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya gode wa gwamnatin Faransa bisa jajircewa da goyon bayi ga Kano, yana mai cewa gwamnati za ta ci gaba da aiwatar da tsare-tsaren da za su tabbatar da ruwan sha mai inganci ga al’umma.

Ya ƙara da cewa Jihar Kano za ta ci gaba da daidaita ayyukanta da manufofin ƙasa ta hanyar ƙarfafa hukumomi, inganta gaskiya da bai wa jama’a ingantattun ayyuka masu ɗorewa.

By ukarofi