Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Asusun tallafawa manyan makarantu na Nijeriya (TETFund) ta ce, ta kashe Naira biliyan 30 a manyan makarantu a faɗin Nijeriya domin ƙarfafa tsaro a Nijeriya daga watan Janairu zuwa yau.
Shugaban asusun, Aminu Masari, ne ya bayyana hakan a cikin wani jawabi da ya fitar a Katsina a ranar Talata.
Masari, wanda ya taɓa zama gwamnan Katsina, ya ce, wannan mataki da suka ɗauka ya taimaka wajen tabbatar da tsaron ɗalibai da lakcarori da sauran mazauna manyan makarantu.
A cewarsa, tallafin samar da tsaron ya yi daidai da manufar Shugaban ƙasa, Bola Tinubu, na samar da kyakkyawan yanayi na koyo da koyarwa a dukkan manyan makarantun kasar nan.
“Kamar yadda muka samar da kasafi don samar da wutar lantarki, shi ne muka ga dacewar mayar da hankali ga samar da tsaro. ɗalibai da malamai suna buƙatar tsaro domin gudanar da ayyukansu,” ya faɗa.
Ya ce, da yawan makarantu sun nemi tallafin samar da fitilun kan titin na sola da gyara katangar makaranta da sauran ayyuka na inganta tsaro.
Ya yaba wa shugaban Nijeriya saboda tallafa wa TETFund, yana mai buga misali da amincewa da ya yi da kaso 50 na kuɗin harajin da Nijeriya ke samu na shekarar 2024.
“Wannan tsari zai fara aiki ne daga watan Janairu wanda zai ƙara bunƙasa ƙarfin asusun wajen gudanar da ayyuka,” ya faɗa.
Shugaban kwamitin amintattun na TETFund ya yi bayanin cewa taron da aka gudanar na kwanakin baya, an yi ne domin wayar da kan masu ruwa da tsaki kan ayyukan asusun da kuma jin ƙorafinsu da yadda za a inganta TETFund.
A cewarsa, wannan taro dama ce ta tattara masu ruwa da tsaki a fannin ilimi a wuri daya da ‘yan majalisu da ƙungiyar malaman jami’a ta ƙasa da shugabannin jami’o’i da ɗalibai da sauransu.
“Mun yi musayar ra’ayoyi da jin shawarwari da yadda za mu yi aiki tare domin inganta ayyukan TETFund wajen shigo da kowa da kowa da samar da tsare-tsare da sauran al’amuran da suka shafi mayan makarantu,” ya bayyana.
Ya ƙara da cewa, an yi amfani da taron wajen tattauna muhimman matsalolin da ake fama da su da nufin ɗaga likkafar manyan makarantun ta yadda za su yi gogayya da takwarorinsu na duniya a fannin bincike da samar da ma’aikata da samar da ayyukan more rayuwa.
Ya ce samar da tsaro a manyan makarantun na zuwa ne a lokacin da ‘yan ta’adda ke zafafa hare-harensu kan makarantun sakandare da wuraren ibada da gonaki a Nijeriya.
