Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce ta samu ƙorafe-ƙorafe har 83,776, kuma 621 da ta warware sun dangancin aure ne a shekarar 2024.
Kwamandan rundunar, Sheikh Amin Ibrahim Daurawa, ne ya bayyana hakan yana mai cewa hukumar ta samu cigaba tun bayan zuwan gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf a ranar 29 ga Mayun 2023.
Ya ce, hukumar ta farfaɗo da ayyukanta masu yawa ciki har da lalata dubunnan kwalaben barasa bayan samun umarnin kotu kamar yadda jaridar Kadaura24 ta rawaito.
Rundunar ta kuma yi nasarar musuluntar da mutane da dama tare da raba tallafi daga irin kuɗaɗen da ta tattara haɗi da bashin Naira biliyan 212,334,839 da ta ƙwato daga masu taurin bashi da aka shigar mata da ƙorafi a kansu.
Sauran ayyukan da hukumar ta yi sun haɗa da: auren gata ga ma’aurata 3,800 da horas da jami’anta 1,000 da raba kayan tallafi ga marayu da gajiyayyu.
Sheik Daurawa ya ce, hukumar na da jami’ai sama da 12,436 a ƙananan hukumomi 44 na Kano.
Sannan hukumar na da sashen mata ‘yan Hizba da ke ƙarƙashin jagorancin Dr. Khadija Sagir Suleiman, da yawansu ya kai 2,362.
Daurawa ya ce gwamnatin na shirin ɗaukar matakai na inganta ayyukan hukumar ta hanyar samar da makarantar horar da jami’an Hizba da ƙara wa ma’aikatan albashi da fidda tsarin ritaya da samar musu da kayan aiki.
Sannan ya ce, gwamnan tin na da shirin samar wa da hukumar sabuwar shalkwatar da nufin ƙarfafa mata guiwa wajen cigaba da tabbatar da adalci da zaman lafiya a jihar Kano.
