Kano: ‘Yan daba sun kai hari rumfar zaɓe a Kurna

‘Yan daba sun kai hari rumfar zaɓe mai lamba 030 cikin Gundumar Alasawa Kwaciri, Kurna Gabas a yankin Ƙaramar Hukumar Fagge, Jihar Kano.

Bayanai sun ce sun kai harin ne ɗauke da makamai tare da tarwatsa masu zaɓe inda kowa ya tsere neman mafaka.

An yi sa’a ‘yan sanda a yankin sun yi aikinsu wajen kwantar da tarzomar inda suka kora ‘yan dabar da kuma bai wa jama’a da ma jami’an zaɓe kariya kana aka ci gaba da zaɓe yadda aka tsara.

Sai dai babu wanda ya jikkata sakamakon harin.

A ranar Asabar Hukumar Zaɓe, INEC, ta gudanar da zaɓen cike giɓi a wuraren da lamarin ya shafa a sassan ƙasa don kammala zaɓe a yankunan.