Kano za ta saka wa Tinubu da ruwan ƙuri’u a 2027 — Barau Jibrin

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya ce mutanen Jihar Kano za su rama kyakkyawar alherin da Shugaba Bola Tinubu yake nunawa gare su da zaben sa da kuri’u masu yawa a zaben 2027 mai zuwa.

Sanata Barau, wanda ke wakiltar Mazabar Kano ta Arewa a majalisar dattawa, ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin ƙaddamar da Shirin Tallafin Karatu ga Dalibai ƙarƙashin gidauniyarsa, a Jami’ar Yusuf Maitama Sule, Kano.

Ya bayyana cewa ɗaya daga cikin muhimman ayyukan da Shugaba Tinubu ya yi wa Kano shine amincewa da haɓaka Kwalejin Ilimi ta Tarayya zuwa Jami’ar Ilimi ta Tarayya, wadda aka kuma sa wa suna Alhaji Yusuf Maitama Sule, ɗan siyasa kuma dattijo mai daraja.

Mataimakin shugaban majalisar dattawan ya ce ƙoƙarin ganin wannan haɓakawa ta tabbata ya ɗauki kusan shekaru goma, amma amincewar da Shugaba Tinubu ya bayar cikin gaggawa ta nuna yadda gwamnatinsa ke da niyyar ƙarfafa ci gaban ɗan adam ta hanyar ilimi. Ya ƙara da cewa kulawar Shugaba Tinubu wajen gina ababen more rayuwa da kula da mutane musamman a Arewacin Nijeriya ta bayyana sosai a cikin yawan mukamai da ayyukan raya ƙasa da ake gani a yankin.

A wani ɓangare na shirin nasa na tallafawa ilimi, Sanata Barau ya sanar da bayar da guraben tallafin karatu ga dukkan daliban Kano Arewa da ke karatu a jami’ar, tare da alƙawarin faɗaɗa wannan taimako zuwa sauran sassa na jihar.

A cewarsa:  “Ina so in gode wa Shugaban ƙasa, shugaban da muke alfahari da shi, shugaban da yake son Kano, wanda yake son Arewacin Nijeriya da ƙasar nan baki ɗaya. Ya amince da buƙatar mu ta dogon lokaci don haɓaka wannan makaranta zuwa jami’a, kuma saboda haka muna godiya ƙwarai.

“Ba mu taɓa neman wani abu daga Shugaban ƙasa muka ji ‘a’a’ ba. Don haka, me zai hana mu so Shugaban ƙasa? Dole mu saka masa, kuma muna jiran lokacin yin hakan a shekarar 2027.”

By ukarofi