Kansiloli sun tsige Mataimakin Shugaban Ƙaramar Hukuma a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina

Kansilolin Ƙaramar Hukumar Malumfashi guda 9 cikin 12 sun gudanar da wani zama na musamman tare da tsige Shugaban Majalisar, Hon. Abdullahi Rabi’u mai wakiltar mazaɓar Yaba da mataimakin shi, Hon Mustapha Ma’azu mai wakiltar mazaɓar Gorar-Dansaka.

Haka zalika kamar yadda ɗaya daga cikin kansilolin ya shaida wa Blueprint Manhaja, kansiloli sun kuma tsige Mataimakin Shugaban Ƙaramar Hukumar ta Malumfashi, Hon Abdulrazak Tukur Maifada bisa zarge-zargen aikata ba daidai ba.

Daga bisani kansilolin sun naɗa sababbin shuwagabannin kamar haka:- Hon. Salmanu Saminu a matsayin Shugaban Majalisar; Hon. Ibrahim Muhammed Rahimi (Yammama Ward) a matsayin Mataimakin Shugaban Majalisar, sai Hon. Mustapha Ma’azu a matsayin Shugaban masu Rinjaye.

Bayan naɗa sabbin shugabannin, majalisar ta naɗa Hon Hamisu Muhammed (Nababa) a matsayin Mataimakin Shugaban Ƙaramar Hukumar na rikon ƙwarya.