Daga MOHAMMED ALI a Gombe
Ɗa ga shahararren mawaƙin Hausan nan, Marigayi Alhaji Musa Ɗanƙwairo, wato Alhaji Ibrahim Musa Ɗankwairo, ya gargaɗi matasa, da kar su kuskura su bada kai ga wasu ‘yan siyasa waɗanda buqatarsu kawai, su ci zaɓe, su yi watsi da su matasan, bayan sun yi amfani da gumin su.
Ibrahim Ɗanƙwairo, wanda shi ne Sarkin Samarin garin Tafa dake Ƙaramar Hukumar Kagarko ta jihar Kaduna, ya yi wannan gargaɗin ne yayin hira da ‘yan jarida a garin Tafa a ranar Lahadin da ta gabata, lokacin wani taron tallafa wa matasa da ya yi.
A cewar shi, matasa sune ginshiƙin rayuwar al’umma, don haka, dole ne zamani ya tafi tare da su, kuma gwamnati ta yi duk iya yinta, ta taimaka musu da aikin yi, ko sana’o’i, ko basu jarin yin kasuwanci domin dogaro da kai, baya ga irin tasu gudunmawar da suke ba su (matasa).
Sai ya ja kunnuwan matasan garin Tafa, da ma wasu a faɗin Arewaci, da su kawo ƙarshen al’adar nan ta shaye-shaye da bangar siyasa, wanda ‘yan siyasa masu neman kujerar mulki kawai, ke amfana da ita, su bar matasan da shan ƙura.
“Saboda haka, Ina kira ga dukkan matasa masu kishi, su nuna ‘yancin su a zaɓen 2023 mai zuwa, su fito ƙwansu da ƙwarƙwatarsu, su kaɗa ƙuri’o’in su don zaɓen adilan shugabanni waɗanda za su kai su ga tudun ‘mun tsira’, amma ba kawai, su bada kai a maishe su ‘yan bangar siyasa ba. Su adana katin zaven su da kyau su kuma haɗa kawunansu, saboda idan baka da katin zaɓe da kai da wanda bai zo duniya ba duk ɗaya kuke.”
Sai Ibrahim Ɗanƙwairo ya yaba wa matasan saboda, baya ga amfani da basirar da Allah ya ba su, suna kuma aikin halak don dogaro da kansu, suna kuma ci gaba da bashi goyon baya, yana mai ƙarawa da cewa, ya tallafa wa ɗimbin matasa waɗanda yawan su ba su lissafuwa tun zuwan shi garin Tafa shekaru 25 da suka wuce.
Ya ce, shi ne ya fara gina wurin koyon sana’a ta matasa a garin, da kuma gina makaranta ta farko a garin (Private School) kuma yara na ɗaukan darasi a kyauta. Har ila yau, ya ce ya bubbuɗe wuraren koyon sana’a don mata musamman da kuma cibiya don ilmantar da matasa a kan illolin shaye-shaye da wasu aikin assha, kuma a cewar shi, hakan ya kawo nasarori ba iyaka a garin.
“Ni ne kuma na fara gina gidan saukan baƙi a Tafa, inda kamilallun mutane ke sauka, saɓanin a can baya sai gidajen karuwai kawai,” inji shi.
Sarkin Matasan wanda haifaffen Anguwar Gidan Kano ne dake cikin Ƙaramar Hukumar Maradun ta Jihar Zamfara, ya ce duk ilmin sa daga firamare zuwa sakandare, a Sifawa da Farfaru ya yi su, banda Shehu Shagari College of Education Sokoto, inda ya samu shaidar kammala karatu na NCE a fannin harshen Hausa da Arabiyya.
Ya ƙara da cewa, ya yi aikin malanta, kiɗa da waƙa, kafin daga bisani, ya shiga harkar kasuwanci da noma, sana’o’in da ya ce, sun qara mishi ƙwarin gwiwa wajen taimakon al’umma, musamman matasa.
Sai ya shawarci al’umma, su ci gaba da yi wa gwamnati da ƙasa baki ɗaya addu’a, don Allah ya kawo ƙarshen masifun rashin tsaron da Nijeriya ke fuskanta yanzu, ya kuma jinjina wa jami’an tsaro da suke aiki tuƙuru don cin nasara. Ya kuma yi godiya ga DPO da ‘yan sanda da sauran masu sa kai, don kawo zaman lafiya a Tafa da ƙasa bakiɗaya.
