
Shugaba Bola Tinubu ya tabbatar da cewa zai halarci taro Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya (UN General Assembly) karo na 81 da za a gudanar a watan Satumba.
Ana sa ran Shugaba Tinubu zai gabatar da jawabi a gaban shugabannin ƙasashe da wakilan duniya, inda zai yi bayani kan sauye-sauyen da gwamnatinsa ta aiwatar da kuma irin nasarorin da Nijeriya ta samu a fannonin tattalin arziki, gudanar da mulki da sauran muhimman gyare-gyare.
Taron na ɗaya daga cikin manyan tarukan duniya da ke haɗa shugabannin ƙasashe domin tattauna batutuwan da suka shafi zaman lafiya, tsaro, ci-gaban tattalin arziƙi da haɗin-gwiwa tsakanin ƙasa-da-ƙasa.
Haka kuma, shugaban ƙasar na sa ran amfani da wannan dama wajen bayyana matsayin Nijeriya akan muhimman batutuwan duniya tare da ƙarfafa dangantakarta da sauran ƙasashen duniya.
