Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
A yayin da kashe-kashen mutane ke ci gaba da ƙaruwa a jihar Benue, Gwamnan jihar, Reɓerend Father Hyacinth Alia, ya bayyana cewa abinda mutanen Benue ke buƙata shi ne cikakken goyon bayan Gwamnatin Tarayya, ba ayyana dokar ta-ɓaci ba.
Da yake magana a shirin “The Morning Show” na Arise a ranar Laraba, Gwamna Alia ya ce matsalar rashin tsaro a jihar Benue ba ta fi ƙarfinsa ba, sai dai yana buƙatar taimakon Gwamnatin Tarayya domin shawo kan rikicin.
Ya ce gwamnatinsa tana da ƙarfin magance kashe-kashen da ake yi a jihar, amma yana buƙatar ƙarin goyon baya domin korar makiyayan da ke kai hare-hare a cikin al’ummomin jihar Benue.
Ya ce, “Abinda muke buƙata yanzu taimakon gaggawa ne. Muna buƙatar cikakken goyon baya. Gwamnatin Tarayya na tare da mu. Sun turo tankokin yaƙi guda biyu. Hakan ya sauya yanayinmu. Labarin ya fi kyau yanzu, amma abinda ya kamata mu yi shine dawo da mutanenmu gida, mu kori mamayen da ke ɗauke da makamai, waɗanda har ba su ma iya harsunan Nijeriya da muke amfani da su ba. Ya kamata su koma inda suka fito, su bar mu manoma mu koma gonakin kakanninmu. Babu buƙatar ayyana wata dokar ta-ɓaci a nan.”
