Kashe-kashen Filato: Hakan ba zai sake faruwa ba, inji Tinubu ga iyalan waɗanda iftila’in ya afka wa

Spread the love

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ci alwashin cewa ba za a sake ganin tashin hankalin da aka gani a garin Jos da ke Jihar Filato ba.

Tinubu ya bayyana haka ne a lokacin da ya ziyarci jihar domin yi wa jama’ar jihar jaje musamman ga iyalan waɗanda iftila’in ya shafa.

Shugaban wanda ya gana da masu ruwa da tsaki na jihar a tashar jiragen saman Heipang, ya ce za su yi iya bakin ƙoƙarin su domin tabbatar da zaman lafiya a Jihar.

Shugaban Tinubu da ya ziyarci jihar da misalin karfe 5 na yammacin yau, a kan hanyar ta zuwa hutu a Lagos, ya bayyana aniyarsa na ganin birnin Jos ya dawo da kimar sa kamar yadda aka san shi a da lokacin da suke tasowa.

“Ina muku alkawarin cewar, abinda ya faru ba zai sake faruwa ba. Na san raɗaɗin da kuke ji, Na kalla a bidiyo yadda mahaifiyar Ayuba ki ka rungume shi da kuma irin raɗaɗin dake fuskarki, amma Ubangiji ne kawai zai faranta miki rai, babu yawan kudin da zai mayar muku da asarar da kuka yi.”

Ya cigaba da cewa, “A matsayin mu na gwamnati za mu yi iya bakin ƙoƙarin mu domin jajanta muku da kuma faranta muku rai, amma maganin wannan matsala ita ce Jos ta koma matsayin ta na Jos, wanda mutane irin mu suka sani lokacin da muka ta shi.”

Gwamnan jihar, Caleb Mutfwang wanda ya tarbi Tinubu, ya bayyana farin cikin sa da damuwar da shugaban ya nuna game da lamarin, da kuma irin goyan bayan da yake ba su domin tinkarar matsalar.

Mutfwang ya kuma nemi bai wa tawagar jihar wani lokaco domin zuwa Abuja ganawa da shugaban la’akari da cewar ziyarar ta yau ta ɗan gajeren lokaci ne, kuma akwai batutuwa da dama da suke buƙatar tattaunawa da shugaban.

By Babaji