Akwai yiwuwar ɗan tsohon shugaban ƙasa Buhari ya tsaya takarar ɗan majalisar tarayya

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

Rahotanni sun bayyanawa cewa gwamnan jihar Katsina, Dikko Umar Raɗɗa ya amince da Yusuf Buhari ɗan tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a matsayin wanda zai yi wa jam’iyyar APC takarar ɗan majalisar tarayya a mazaɓar Daura, Mai ‘adua da Sandamu.

Bayanin haka na ƙunshe cikin wani taro na masu ruwa da tsaki na Jam’iyyar APC a ƙaramar hukumar Sandamu ta jihar Katsina, ‘yan jam’iyyar sun nuna muhimmancin ƙarfafa haɗin kan jam’iyyar APC kafin zaɓen 2027, saboda haka ne suka goyi bayan Yusuf Buhari, ɗan tsohon shugaban Najeriya Muhammad Buhari, a matsayin wanda aka fi so ya tsaya takarar mazabar ɗan majalisar tarayya ta Daura/Sandamu/Mai’adua.

An yanke wannan shawara ne a wani babban taro da aka gudanar a sakatariyar ƙaramar hukumar Sandamu, wanda ya haɗa zaɓaɓɓun jami’an jam’iyyar da kuma ‘yan siyasa a faɗin mazaɓar tarayya.

A lokacin da yake jawabi ga mahalarta taron, shugaban ƙaramar hukumar, Usman Na Lado, ya bayyana amincewa da takarar a matsayin ƙuduri na ɗaukacin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar wanda ke da nufin ƙarfafa damar da jam’iyyar ke da ita a zaɓen.

Shugaban ƙaramar hukumar ya ƙara da cewa an ɗauki takarar Yusuf Buhari a matsayin wadda ta dace bisa ga yadda yake da dama da kuma karɓuwa a tsakanin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar.

Ya ƙara da cewa bayan kujerar Majalisar Wakilai, taron ya kuma sake jaddada goyon bayansa ga shugaba Bola Tinubu da gwamna Dikko Umar Raɗɗa a matsayin waɗanda jam’iyyar za ta tsayar a matsayin shugabanninta na kujerun shugaban ƙasa da na gwamna, a babban zaɓen 2027.

Ya kuma bayyana cewa masu ruwa da tsaki sun kuma goyi bayan Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Katsina, Nasiru Yahaya Daura, a matsayin ɗan takarar kujerar Sanata ta Daura, inda ya ƙara da cewa goyon bayan ya nuna shirye-shiryen da suka yi tun farko na babban zaɓen 2027, yana mai kira ga ‘ya’yan jam’iyyar da su ƙara himma wajen wayar da kan jama’a.

Majiyar Blueprint Manhaja ta jaridar Daily Trust ta ce, wasu majiyoyi a cikin jam’iyyar sun bayyana cewa amincewa da Yusuf Buhari umarni ne bayyananne daga gwamna Raɗɗa.

A cewar majiyar, Yusuf Buhari shine ɗan takarar da gwamna Raɗɗa ya amince da shi.

By ukarofi