Majalisar Dokokin Katsina ta yi kira ga gwamnatin Jihar kan aikin wutar lantarki a Charanchi

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Kiran ya biyo bayan sake kai ƙuduri akan neman gwamnati ta cigaba da aikin wutar lantarki a mazaɓar Dan Makwaro ‘A’ da Dan Makwaro ‘B’, Tsakatsa da kuma Rugar Wake, da ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Charanchi Hon. Lawal Isah Kuraye, a karo na biyu a gaban majalisar.

A inda ya bayyana cewa, wannan aiki ya kai kimanin shekar 9 ana wannan aiki sai an fara sai a tsaya don haka yake sake kira ga gwamnati da ta dubi wannan al’umma na wannan mazaɓu don a cigaba da wannan aiki.

Saboda muhimmacin wannan ƙuduri yasa sauran ‘yan majalisa suka nemi da a sanya ƙananan hukumomin su acikin wannan aikin.

Bayan doguwar muhawara, sauran yan majalisa sun goyi bayan wannan ƙuduri.

Daga ƙarshe kakakin majalisar Rt.Hon. Nasir yahaya Daura,ya bayar da umarni a miƙa wannan kudirin zuwa ga ɓangaren zartaswa domin a ɗauki matakin da ya dace.

By ukarofi