Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Samamen, da aka fara ya shafi wurare da dama ciki har da tashar mota da manyan hanyoyi inda jami’an hukumar suka gargaɗi masu gudanar da ayyuka a wuraren su koma tashoshin da aka amince da su.
Jami’an hukumar sun kuma gargaɗi masu sayar da kayayyaki a kan tituna da masu wankin motoci da babura, suna mai cewa irin waɗannan ayyuka na haddasa cunkoso, toshe hanyoyin masu tafiya a ƙafa, da kuma lalata kwalta.
Babban daraktan KASSAROTA, Manjo Garba Yahaya Rimi (mai ritaya), ya ce an ɗauki matakin ne bayan gargaɗi da dama da aka sha yi masu amma biris.
Ya ƙara da cewa hukumar ta ƙwace wasu kayayyaki daga waɗanda suka ci gaba da karya dokar.
Ya jaddada cewa hukumar za ta ci gaba da gudanar da irin wannan samame lokaci zuwa lokaci domin tabbatar da tsafta, tsaro da sauƙin zirga-zirga a faɗin jihar.
