Gwamna Raɗɗa ya buɗe masallacin Juma’a da mataimakinsa ya gina a Ƙanƙara

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnan Katsina, Malam Dikko Raɗɗa, ya ƙaddamar da buɗe sabon katafaren masallacin Juma’a da mataimakin gwamnan Jihar, Hon. Faruk Lawal Joɓe, ya gina a garin Ƙanƙara.

Ranar juma’a da ta gabata gwamnan ya samu wakilcin sakataren gwamnatin Jihar Katsina, Abdullahi Garba Faskari ya buɗe masallacin.

Masallacin, wanda aka gina a fili mai tsawon mita 200 da faɗin mita 200, an yi shi da tsarin gine-ginen zamani tare da kyawawan kayayyakin ƙawa. Haka kuma, masallacin yana da sashi na musamman domin mata.

Taron buɗe masallacin ya samu halartar manyan baƙi daga ciki da wajen Jihar Katsina, ciki har da mataimakin gwamnan Jihar Yobe da shugaban jam’iyyar APC na Jihar Katsina, Dr. Bishir Gambo Saulawa.

Sauran waɗanda suka halarta sun haɗa da Kakakin majalisar dokokin Jihar Katsina, Rt. Hon. Nasir Yahaya Daura; Babban Alƙalin Jihar Katsina, Mai Shari’a Musa Danladi Abubakar; da mambobin majalisar dokoki da na zartarwa ta Jihar.

Haka kuma, manyan sarakuna da malaman addini sun halarci taron, ciki har da sarkin Katsina, Alhaji Abdulmuminu Kabir Usman, wanda ya samu wakilcin ƙauran Katsina, Alhaji Aminu Abdulkadir.

A yayin taron, wakilin sarkin Katsina ya sanar da naɗin sabon limamin masallacin.

By ukarofi