Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
A wani taro da aka gudanar a makarantar makafi a Katsina, an rabawa ɗalibai kayayyakin karatu da gwamnati ta samar domin tallafa musu wajen samun ingantaccen ilimi.
Kayayyakin da aka raba sun haɗa da katifu, rigunan karatu, takardun A4 da kuma kayan karatun Braille, waɗanda aka tanada domin taimaka wa ɗaliban da ke da buƙata ta musamman su samu damar cigaba da karatunsu cikin sauƙi.
A yayin taron, da yake jawabi, sarkin makafi, Alhaji Garba Nahuta, ya bayyana godiya ga Gwamnan jihar malam Dikko Raɗɗa bisa wannan tallafi da ya samar domin inganta harkar ilimi a makarantar, ya ce wannan aiki ya nuna cewa gwamnatin jihar na kula da dukkan al’umma ba tare da nuna bambanci ba.
Haka kuma ya miƙa godiya ga kwamishinan Ilimi wanda ya bayar da dama aka aiwatar da wannan shiri, ya bayyana cewa da ba a samu wannan dama ba, watakila ana iya gudanar da irin wannan aiki a wasu makarantu a manta da wannan makaranta ta masu buƙata ta musamman.
Ya kuma yi godiya ga babban sakatare na ma’aikatar ilimin firamare da sakandare ta jihar, inda ya bayyana ta a matsayin mace mai son taimakon al’umma musamman masu buƙata ta musamman.
Bugu da ƙari, ya yaba da ƙoƙarin shugaban makarantar, bisa yadda yake ƙoƙarin tafiyar da makarantar da kuma tabbatar da ci gabanta.
Shi ma a jawabin sa, Shugaban makarantar, Malam Lawal Jibril, ya ce gwamnan jihar Katsina, na taka rawa sosai don ganin makarantar ta amfana da kayan aiki don ƙarfafa ilimin ɗaliban.
Ya ce taimakon da akai ma makarantar, ana iya tsawon shekaru ana amfani da su ba su lalace ba, ya ce abin a yaba ne yadda gwamnatin jihar ta samar da kaya masu inganci a makarantar kyauta ga ɗaliban.
Haka kuma, ya ambaci wasu manyan mutane da ke nuna kulawa da makarantar ciki har da Sanata Abdul’aziz Musa Yar’Adua, wanda ya ce ko cikin kwanakin nan ya ziyarci makarantar, domin bada gudunmawa kan ayyukan da ake yi na tallafawa ɗaliban, ya kuma jaddada cewa, Mai Shari’a alƙalin-alƙalai na jihar Katsina, Alhaji Musa Danladi, yana daga cikin waɗanda ke nuna kulawa da wannan makaranta.
Ita ma da take jawabi lokacin ƙaddamar da kayan, babban sakatariya Hajia Ummul Khairi Ahmed Bawa, wanda ta wakilci jwamishinan Ilimi a matakin farko da na sakandare, Hon. Suleiman Yusuf, ta bayyana cewa, gwamnatin jihar Katsina ba ta gajiya da hidima ga al’ummarta musamman a ɓangaren ilimi.
Ta ce daga cikin makarantun da aka ware domin tallafa masu kan inganta ilimin su, Gwamnatin jihar Katsina ba ta mance da makarantar makafi ba a jihar, shiyasa aka zo don miƙa ma su kayan su ga shugaban makarantar.
A ƙarshe, an yi kira ga hukumomin makarantar da su tabbatar an yi amfani da kayayyakin da aka kawo yadda ya kamata, tare da kula da su domin kada su lalace ko su ɓace.
