Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Kwamitin Majalisar Dattawa kan Asusun Jama’a ya gayyaci tsofaffin shugabannin Kamfanin Man Fetur na ƙasa (NNPCL), ciki har da tsohon Babban Darakta na rukunin kamfanin, Mele Kyari, domin amsa tambayoyi kan wani zargin giɓin kuɗi da ya kai kimanin Naira tiriliyan 210 a cikin rahotannin kuɗaɗen kamfanin da aka tantance daga shekarar 2017 zuwa 2023.
Shugaban kwamitin kuma Sanata mai wakiltar Nasarawa ta Yamma, Sanata Aliyu Wadada, ne ya bayyana hakan yayin wata ganawa da manema labarai a harabar Majalisar Dokoki da ke Abuja.
Sanatan ya ce, kwamitin ya fara wannan bincike ne a ƙarƙashin ikon da Kundin Tsarin Mulkin ƙasa ya ba shi domin tabbatar da gaskiya, riƙon amana da kuma yadda ake kashe kuɗaɗen jama’a.
Ya bayyana cewa binciken yana samun goyon bayan tanade-tanaden sashe na 85, 88 da 89 na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na 1999, tare da dokokin tafiyar da harkokin Majalisar Dattawa.
Asalin fara binciken:
Wadada ya ce binciken ya fara ne a watan Mayun shekarar 2025, bayan kwamitin ya lura da wasu kura-kurai a tsarin sarrafa kuɗi yayin nazarin rahotannin Babban Mai Binciken Kuɗaɗen Tarayya (Auditor-General for the Federation) na shekarun da suka ƙare a 2019 da 2020.
Bayan haka, kwamitin ya nemi ƙarin bayanai daga NNPCL, tare da duba cikakkun rahotannin kuɗaɗen kamfanin daga shekarar 2017 zuwa 2023.
Sanatan ya ƙara da cewa, kwamitin ya kuma binciki bayanan kuɗaɗe na tsohuwar Hukumar Kula da Zuba Jari a Harkar Man Fetur ta ƙasa (NAPIMS) wadda a yanzu ake kira Kamfanin Zuba Jari a ɓangaren Haƙar ɗanyen Mai na NNPCL.
A cewarsa, kwamitin ya gabatar da tambayoyi guda 19 domin neman ƙarin bayani kan wasu saɓani da aka samu a cikin rahotannin kuɗaɗen kamfanin, amma amsoshin da aka bayar ba su gamsar da kwamitin ba.
Kwamitin ya ce, ya lura cewa a rahoton kuɗaɗen kamfanin na shekarar 2022 akwai wani adadin kuɗi na naira tiriliyan 103 da aka rubuta a matsayin kuɗaɗen da aka tara a matsayin bashi ko wajibcin biya.
Wadada ya ce, an bayyana cewa kuɗin sun haɗa da kuɗin riƙewa (retention fees), kuɗin shari’a da kuma kuɗin duba lissafi, amma babu takamaiman adadin da aka ware wa kowanne daga cikin su.
Daga baya kamfanin ya bayyana cewa wannan adadi na naira tiriliyan 103 kuɗaɗe ne da abokan hulɗar hazin gwiwa suka kashe a tsarin joint ɓenture cash call. Sai dai Sanatan ya ce wannan bayanin ya saɓa da abin da ke cikin rahoton kuɗaɗen kamfanin.
Ya kuma jaddada cewa an soke tsarin cash call tun a shekarar 2016, wanda ya fara aiki daga Janairun 2017, don haka kwamitin ya ce wannan bayani ba zai karɓu ba.
Baya ga haka, kwamitin ya gano cewa kamfanin ya rubuta wani adadin naira tiriliyan 107 a matsayin kuɗaɗen da ake binsa daga wasu tsofaffin bankuna da sauran kamfanoni zuwa watan Disamban 2023.
Sai dai, a cewar kwamitin, kamfanin bai iya bayyana takamaiman sunayen bankunan ko kamfanonin da ake binsu wannan kuɗi ba.
Haka kuma kwamitin ya lura da abin da ya bayyana a matsayin maimaita cire kuɗin tallafin man fetur har sau biyu, wanda ya kai kusan naira tiriliyan 3.8.
A cewar Wadada, an cire kuɗin tallafin daga kuɗin da aka samu daga sayar da ɗanyen mai a littafan NAPIMS, sannan kuma aka sake cire shi daga kuɗin sayar da man fetur a littafan NNPC.
Kwamitin ya kuma yi tambaya kan wani adadi na naira tiriliyan 5 da aka caje a matsayin kuɗin samar da ɗanyen mai tsakanin shekarun 2017 zuwa 2021.
A cewarsa, NNPC da NAPIMS sun amince sun caje wannan kuɗi, amma kwamitin ya ce abin ba zai yiwu ba domin waɗannan hukumomi ba su da aikin haƙar ɗanyen mai kai tsaye.
Naira biliyan 5.9 na sauya suna:
Wani ɓangare da ya jawo cece-kuce shi ne kuɗin Naira biliyan 5.9 da aka kashe wajen sauya tsarin kamfanin daga NNPC zuwa NNPCL.
Sanatan ya ce NNPC ya kashe Naira biliyan 2.9 daga kuzin sayar da man fetur, yayin da NAPIMS ya kuma caje naira biliyan 2.9 daga kuɗin ɗanyen mai domin wannan manufa.
A cewarsa, hakan ya kai jimillar naira biliyan 5.9 da aka kashe kawai domin sauya sunan kamfanin zuwa sabon tsarin kasuwanci.
Matakan da kwamitin ya ɗauka:
Kwamitin ya yanke shawarar cewa dole NNPCL ya yi cikakken bayani kan jimillar naira tiriliyan 210 da suka ƙunshi naira tiriliyan 103 da naira tiriliyan 107 da ba a iya bayyanawa yadda ya kamata ba.
Haka kuma kwamitin ya umarci kamfanin da ya mayar da duk wasu kuɗaɗen da aka caje a matsayin kuɗin samar da zanyen mai a cikin wannan lokaci.
An kuma gayyaci tsofaffin shugabannin kamfanin, ciki har da Mele Kyari a matsayin tsohon Babban Darakta, Umar Ajiya a matsayin tsohon Babban Daraktan Kuɗi, da kuma Bala Wunti wanda ya taɓa zama Babban Manajan NAPIMS, domin su bayyana gaban kwamitin.
Za su halarci zaman tare da shugabannin kamfanin na yanzu da kuma masu zaman kansu da suka duba rahotannin kuɗaɗen kamfanin.
Bugu da ƙari, kwamitin ya ba da shawarar cewa Babban Mai Binciken Kuɗaɗen Tarayya ya gudanar da cikakken bincike na musamman (forensic audit) kan rahotannin kuɗaɗen NNPCL daga shekarar 2017 zuwa 2023 domin gano gaskiyar lamarin.
Sanata Wadada ya jaddada cewa kwamitin zai ci gaba da aiki tare da hukumomi daban-daban domin ƙarfafa tsarin riƙon amana da gaskiya wajen sarrafa kuɗaɗen jama’a a Nijeriya.
