Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Tsohon Babban Sufeto Janar na ’Yan Sandan Nijeriya, Kayode Egbetokun, ya bayyana cewa hare-haren da kafafen yaɗa labarai suka riƙa kai wa jagorancinsa a lokacin da yake kan shugabanci ba su kasance na bazata ba, sai dai wani shiri ne da wasu masu ruwa da tsaki masu ƙarfi suka ƙulla domin su daƙile gyare-gyaren da ya kawo a rundunar ’yan sanda.
A wani cikakken bayani da ya yi kan lokacin da yake jagorantar Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya, Egbetokun ya ce shugabancinsa ya fuskanci ƙalubale da dama wajen kawar da wasu tsofaffin halaye marasa kyau da suka yi ƙatutu a cikin rundunar, ciki har da yadda wasu jami’ai ke sauya bayanan aikinsu domin su tsawaita shekarun da za su yi a hidima.
Ya bayyana cewa, wasu jami’ai kan biya kuɗaɗe domin a canja bayanan hidimarsu, ta yadda za su ci gaba da zama a cikin rundunar fiye da shekarun ritayar da doka ta tanada. A cewarsa, wannan ɗabi’a ce da ta zama ruwan dare a baya, amma gwamnatinsa ta ɗauki matakai masu tsauri domin kawo ƙarshenta.
Egbetokun ya ce ba wai dakatar da wannan halin kawai suka yi ba, har ma sun gano waɗanda suke da hannu a ciki, inda aka miƙa sunayensu ga Hukumar Kula da Ayyukan ’Yan Sanda ta ƙasa domin a ɗauki matakin ladabtarwa a kansu.
A cewarsa, dukkan jami’an da aka tabbatar da laifinsu an cire su daga cikin tsarin rundunar bayan bin hanyoyin hukuma da doka ta tanada.
Har ila yau, tsohon shugaban ’yan sandan ya ce wata matsala mai zafi da ta taso a lokacin mulkinsa ta shafi wasu jami’an da aka ɗauka a matsayin ’yan sanda masu koyon aiki (cadets), waɗanda suka nemi ci gaba da zama a hidima fiye da lokacin da doka ta tanada.
Ya ce, jami’an sun dogara da wani hukunci da Kotun Masana’antu ta ƙasa ta yanke domin kare matsayinsu. Sai dai binciken da rundunar ’yan sanda ta gudanar daga baya ya gano wasu manyan kura-kurai a cikin lamarin.
Egbetokun ya bayyana cewa hukuncin kotun ya ta’allaƙa ne da wani saƙo na hukuma (signal) da aka ce ya fito daga Ofishin Sakataren Rundunar ’Yan Sanda, wanda aka ce ya wuce ta hannun Hedikwatar Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Sakkwato.
Sai dai bayan ƙarin bincike, an gano cewa saƙon da aka gabatar a kotu ƙirƙira ce kawai, ba daga ofishin da aka ambata ya fito ba.
Ya ce, sakamakon binciken ya nuna cewa babu wani irin saƙo da ya fito daga ofishin Sakataren Rundunar, kuma har da wanda aka ce an wuce ta hedikwatar ’yan sanda ta Sakkwato — duk an gano cewa ƙirƙirarru ne.
A cewarsa, an miƙa rahoton binciken ga Hukumar Kula da Ayyukan ’Yan Sanda ta ƙasa, wadda ta ɗauki matakan ladabtarwa kan waɗanda aka samu da hannu a cikin lamarin.
Yayin da yake waiwayar salon jagorancinsa, Egbetokun ya jaddada cewa abin da ya bambanta mulkinsa da wasu da suka gabata shi ne yadda ya mayar da hankali kan tsauraran matakan ladabtarwa a cikin rundunar.
Ya ce, ba zai yiwu ’yan sanda su tilasta bin doka ga al’umma ba idan su kansu ba su tabbatar da bin doka da oda a cikin tsarin su ba.
“Ba za mu iya tilasta bin doka yadda ya kamata ba idan ba mu tabbatar da ladabtarwa a cikin rundunarmu ba,” inji shi.
Haka nan tsohon shugaban ’yan sandan ƙasar ya kuma yi zargin cewa wasu attajirai da matakan ladabtarwar suka shafa sun ɗauki nauyin wasu yaƙe-yaƙen kafafen yaɗa labarai domin ɓata masa suna.
