Kasuwar hannun jari ta samu ribar tiriliyan N8.137 a Nijeriya

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Kasuwar hannayen jari ta Nijeriya ta sake nuna ƙarfi a makon da ya gabata, inda masu zuba jari suka samu ribar da ta kai Naira tiriliyan 8.137 sakamakon tashin da manyan ma’aunai suka yi a kasuwar.

Alƙaluman da aka fitar sun nuna cewa ma’aunin Kasuwar Jannun Jari (NGɗ) ya ƙaru da kashi 6.95 cikin ɗari, inda ya rufe makon a maki 194,989.77, yayin da jimillar darajar kasuwa ta tashi zuwa naira tiriliyan 125.164.

A makon da ya gabata, an rufe kasuwar a maki 182,313.08 da darajar tiriliyan 117.027, lamarin da ke nuna gagarumin ci gaba a cikin kwanaki bakwai kacal.

Wannan ƙarin ya bai wa masu zuba jari riba mai yawa, yana ƙara ƙarfin gwiwa a kasuwar da ta daɗe tana fuskantar sauye-sauye sakamakon matsin tattalin arziki.

Dukkan sauran manyan ma’aunai sun rufe makon cikin yanayi na ƙaruwa, sai dai NGɗ Growth Indeɗ wanda ya faɗi da kashi 15.06 cikin ɗari, yayin da NGɗ Sovereign Bond Indeɗ ya tsaya cak ba tare da wani sauyi ba.

A ɓangaren hada-hadar ciniki, an yi musayar hannayen jari guda biliyan 7.662 da darajarsu ta kai naira biliyan 252.566 cikin hada-hada 345,118. Wannan ya fi adadin makon baya, inda aka yi musayar hannayen jari biliyan 4.652 kacal da darajar naira biliyan 193.326 cikin hada-hada 286,751.

ɓangaren harkokin kuɗi ne ya jagoranci hada-hadar kasuwa, inda aka yi cinikin hannayen jari biliyan 5.625 da darajarsu ta kai naira biliyan 113.599 cikin hada-hada 129,729. Wannan ya wakilci kashi 73.41 cikin dari na jimillar yawan hannayen jari da aka yi ciniki da su, da kuma kashi 44.98 cikin dari na darajar kuɗaɗen da aka zuba.

ɓangaren ayyuka (Services Industry) ya biyo baya da hannayen jari miliyan 493.131 da darajarsu ta kai naira biliyan 5.866, yayin da ɓangaren mai da iskar gas ya zo na uku da hannayen jari miliyan 425.657 da darajarsu ta kai naira biliyan 35.742.

Manyan kamfanonin da suka fi ɗaukar hankalin masu zuba jari sun haɗa da FCMB Group Plc, Access Holdings Plc da Zenith Bank Plc, inda aka yi musayar hannayen jari biliyan 3.594 da darajarsu ta kai naira biliyan 69.147. Wannan ya wakilci kusan rabin yawan cinikin da aka yi a kasuwar.

A jimlace, kamfanoni 71 sun samu ƙarin farashi a makon, kasa da 79 da suka karu a makon baya. Sai dai kamfanoni 41 sun faɗi farashi, sama da 27 da suka faɗi a makon da ya gabata, yayin da 36 suka tsaya a matsayinsu ba tare da sauyi ba.

Daga cikin kamfanonin da suka fi samun riba sun haɗa da Zichis Agro Allied, Japaul Gold ɓentures, Infinity Trust Mortgage Bank, Fortis Global Insurance da Jaiz Bank. A gefe guda kuma, RT Briscoe, Mecure Industries, Tripple Gee, Sovereign Trust Insurance da Ellah Lakes su ne suka fi faɗuwa a farashi.

A wani ci gaba mai muhimmanci, NGɗ ta sanar da masu lasisin ciniki cewa an jera takardun bashin kasuwanci na Dangote Cement Plc — Series 1 na naira biliyan 19.9 da Series 2 na naira biliyan 99.9 — ƙarƙashin shirin fitar da takardun bashin da darajarsu ta kai naira biliyan 500, a ranar Laraba, 18 ga Fabrairu.

Masana na ganin cewa wannan gagarumin tashin kasuwa alama ce ta farfaɗowa da ƙaruwar kwarin gwiwa daga masu zuba jari, duk da ƙalubalen tattalin arziki da ake fuskanta a ƙasa.

By ukarofi