Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Kamfanin Mai na Nijeriya (NNPC) da Rukunin Kamfanonin Dangote sun sake ƙulla wani muhimmin ƙawance na dabaru da nufin ƙarfafa makamashi, bunƙasa tace mai a cikin gida da kuma tabbatar da ɗorewar ci gaban tattalin arziki na dogon lokaci.
Wannan sabon mataki ya zo ne bayan wata ziyara ta musamman da Babban Daraktan NNPC, Bashir Ojulari, ya jagoranta zuwa Matatar Dangote da ke Ibeju-Lekki a jihar Legas.
Tattaunawar manyan jami’an ɓangarorin biyu ta kai ga sabunta alƙawarin haɗin gwiwa domin sake fasalta yanayin makamashi a Nijeriya.
A yayin ziyarar, an yi rangaɗi a wuraren aiki tare da mayar da hankali kan ƙarfafa dangantakar kasuwanci da aiki tsakanin NNPC da matatar Dangote.
ɓangarorin biyu sun sake jaddada ƙudurinsu na gina makomar makamashin ƙasa bisa tushen haɗin kai da hangen nesa guda.
Ojulari ya yaba wa Shugaban Rukunin Dangote, Aliko Dangote, kan hangen nesansa da jajircewarsa wajen kammala matatar mai mai ƙarfin tace ganga 650,000 a rana — wani gagarumin aiki da ya ɗora Nijeriya a matsayin babbar cibiyar harkokin tace mai a Afirka.
Ya bayyana cewa, sabon kawancen zai buɗe damammaki masu yawa ta fuskar kadarori, ababen more rayuwa, jari da kasuwanni. A cewarsa, haɗin gwiwar zai ƙara haske da bayyananniyar mu’amala a dukkan hulɗoɗin kasuwanci tsakanin NNPC da Dangote.
Baya ga tace mai, Ojulari ya nuna cewa akwai babbar dama ga kamfanonin biyu su faɗaɗa ayyukansu a ɓangaren haƙar mai, kasuwancin mai, jigilar kaya ta ruwa, samar da iskar gas da sauran fannoni masu alaƙa da makamashi.
Ya kuma nuna godiya ga Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, bisa jagorancinsa a ɓangaren mai da gas, inda ya ce manufofinsa masu ƙarfafa zuba jari da gyaran fuskar ɓangaren sun samar da yanayi mai kyau ga manyan kawance irin wannan su bunƙasa.
A nasa ɓangaren, Dangote ya bayyana cewa al’ummar Nijeriya ne za su fi cin moriyar wannan haɗin gwiwa, domin zai haifar da rage farashi ta hanyar tattalin arziki, tare da buɗe sabbin kasuwanni da samar da ƙarin ayyukan yi.
Ziyarar ta ƙare da ɓangarorin biyu sun sake tabbatar da ƙudurinsu na zurfafa haɗin kai domin tabbatar da tsaron makamashi, bunƙasa masana’antu da kuma samar da ingantacciyar riba ga ƙasa baki ɗaya.
A halin yanzu, NNPC na da kaso 7.25 cikin 100 a matatar Dangote, wani jari da ake kallonsa a matsayin muhimmin mataki na ƙarfafa burinta na faɗaɗa ayyukan tace mai a cikin gida.
