Khadi Inuwa Aminu ya zama Wazirin Zazzau

Daga BASHIR ISAH

Masrautar Zazzau a jihar Kaduna ta naɗa Khadi Muhammad Inuwa Aminu a matsayin Wazirin Zazzau.

Masarautar Zazzau ta tabbatar da naɗin Aminu a matsayin Waziri ne cikin wasiƙar da ta aika masa mai ɗauke da sa hannun Sakataren masarautar, Alhaji Barau Musa (Sarkin Fulanin Zazzau).

Sakataren ya bayyana cikin wasiƙar mai ɗauke da kwanan wata 11 ga Oktoba, 2021 cewa, “Bayan gaisuwa mai yawa. An umurce ni da in sanar da kai cewa, bisa umurnin Gwamnatin Jhar Kaduna ta ranar 20/09/2021 a takardarta mai lamba GHIKD/ 578, Maimartaba Sarkin Zazzau ya tabbatar maka da Sarautar Wazirin Zazzau, kuma Babban Ɗan Majalisar Sarki, daga yau Litini 11/10/2021.”

Ya ci gaba da cewa, “Maimartaba Sarkin Zazzau da al’ummar Masarautar Zazzau suna taya ka murna da fatan alheri, da fatan za ka riƙe amanar Masarautar Zazzau da kawo cigaba da faɗin gaskiya a kowane hali da kuma yin aiki da dokokin Allah (SWT). Muna taya ka murna.”

Kamar yadda wasiƙar ta nuna, naɗin da aka yi wa Khadi Aminu ya soma aiki ne daga ranar Litinin, 11 ga Oktoban 2021.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *