Ki kame kanki ’yar uwa!

A wannan zamani da muka tsinci kawunanmu ciki, mace wacce ta kame kanta daga aikata alfasha da nesantar shiga ta bayyana tsiraici, da qin kula samarin banza bisa hanya, ita ake wa kallon mace mai girman kai.

To duk irin abinda al’ummah za su ce a kanki matuƙar kin kiyaye dokokin Allah, da yin koyi da mata salihan bayi na zamanin Manzon Allah (saww), karki tava damuwa, duk mai ƙaunarki da gaskiya, to ya bi tsarin neman aure yadda addini ya shar’anta domin ke ma’abociyar tsadace.

Bayyana tsiraici alamu ne na fushin Allah, shi ya sa lokacin da Allah ya yi fushi da Annabi Adam da Hauwa sai ya bayyana musu tsiraicinsu.

Wata baiwar Allah ta ke cewa, duk lokacin da na ga mace ta sanya tufafin banza ko kuma tana yawo tsirara sai in tuno iyayenta ya za su yi da faɗinsa Maɗaukakin Sarki: “ku tsayar da su, haƙiƙa su ababen tambaya ne (dangane da amanar da aka basu).”

Ta ce, sai in ƙara jin kunya domin tsoron kar Allah ya tambayi mahaifina da mahaifiyata.

Mafiya yawan ababen da Allah ya haramta a duniya (irinsu giya) ya halatta su a aljannah, amma ban da bayyana tsiraici domin Allah (SWT) cewa ya yi: “haqiqa (ya adam) a cikin aljannah ba za ka ji yunwa ba, sannan kuma ba za ka bayyana tsiraici ba.”

Yana da kyau, a girmama hijabi, da masu sanya hijabi.

Haqiqa hijab lulluvi ne, mai ƙawatah ɗiya mace, ta hanyar rufe surar jikanta, ba tare da bayyana tsiraici, ko bayyana shi ga wanda bai cancanta ba.

Da hakane Allah (SWT), ya yi umurni ta bakin Manzon Allah (SAWW), cewa, matayen Musulmi, su lulluɓe jikinsu da mayafi wadatacce, domin kuɓuta daga zargi, da kare mutunci”.

Amma a yau, hijab ya zama abinda izgili da wulaqantawa tsakanin Musulmi. Wasu sun ɗauke shi tamkar qauyanci da wawanci, alhali sune wawaye ƙauyawa ga karantarwar addinin Musulunci.

Don haka; mata ku killace jikinku domin mazajenku, kuma kada ku tallata jikinku ga wawayen da ba su san darajarku ba.

Iyaye, ku taimaki ’ya’ynku wajen yi musu tarbiyya ta gari, domin wallahi sai Allah ya tambayeku dangane da amanar da aka ba ku ta ’ya’yanku.

Haƙƙin da ya ke kanka ka fara sauke shi kafin ka nemi wanda za a baka a matsayinka na uba. Allah ya sa mu dace.

Daga Fatima Ma’asuma, 09070905293 (tes kawai).