Kiciniyar tikitin mataimakin Tinubu a Arewa maso Yamma

*Gwamnonin yankin sun shiga ganawa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Jagororin Jam’iyyar APC mai mulkin Nijeriya na shiyyar Arewa maso Yamma sun naɗa tawagar wakilai da za su je su gana da ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, game da zaƙulo wanda zai zame masa mataimaki a babban zaɓen 2023 mai ƙaratowa. 

An cimma wannan matsayar ne a wurin taron jagororin shiyyar Arewa ta Yamma, da suka haɗa da gwamnoni, ‘yan takarar gwamna, ministoci da sauransu, wanda ya gudana jiya a Abuja.

A wata sanarwa da mataimakin shugaban APC na Arewa ta Yamma, Salihu Lukman, ya fitar ranar Alhamis, ya ce taron ya yi na’am da fara tarukan neman shawarwari don ƙara ƙarfafa APC a yankin.

A cewarsa, gwamnoni da masu riƙe da ofisoshin siyasa sun ƙara nazari da duba halin da jam’iyya ta tsinci kanta a matakin ƙasa da na shiyyoyi. 

Haka nan sun gano tare da tattara ƙalubalen da APC ke kwana da tashi da su a wasu jihohi, kana suka cimma matsayar ƙara ninka ƙoƙarin da ake na rarrashi da sulhunta juna. 

A sanarwan, Lukman ya ce: “Taron ya tavo gudunmuwar da Arewa maso Yamma ta bayar wajen kafawa da bunƙasar Jam’iyyar APC da kuma nasararta a zave, tare da sanin cewa yankin ne ya samar da kaso 39 na ƙuri’un da APC ta samu a zaɓen shugaban ƙasa na 2015 da 2019.

“Saboda haka shiyyar Arewa ta Yamma ta amince ta tattara buƙatunta da muhimman abun damuwa kuma daga bisani za ta zauna da Tinubu ta baje masa komai ɗaya bayan ɗaya.” 

Jaridar Blueprint ta ruwaito cewa jagororin APC na Arewa maso Yamma sun ɗauki matakin ne yayin da yawon neman shawarwarin masu ruwa da tsaki kan wanda ya dace ya zaɓa a matsayin abokin takara.

Idan za a iya tunawa dai ɗan takarar Jam’iyyar APC ɗin Bola Ahmed Tinubu ya miƙa wa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) sunan Kabiru Masari daga Jihar Katsina a matsayin wanda zai yi masa mataimaki na wucin-gadi bisa wa’adin da hukumar zaɓen ta bai wa jam’iyyun siyasar Nijeriya.