Kirmau Mai Gabas, Sarkin Gaya Marigayi Alhaji Ibrahim Abdulƙadir

Daga AMINA YUSUF ALI a Kano

Mai Martaba Sarkin Gaya da ke Jihar Kano, Alhaji Ibrahim Abdulkadir, ya rasu ne a ranar
Talata, 22 ga Satumba, 2021.

Kirmau mai Gabas shi ne takensa kuma Allah ya amshi abinsa, inda al’ummar Kano, musamman na masarautar Gaya, suka faɗa cikin alhini sakamakon rasuwar Mai Martaba Sarkin Gaya, Alhaji Ibrahim Abdulƙadir.

Sarkin dai ya rasu bayan shafe kusan shekaru 2 yana jinya, wacce aka kasa gane kanta. Ya rasu ya bar mata guda uku; Hajiya Uwani, da Hajiya Ubaida da kuma Fulani Salamatu, snnan kuma  ya bar ‘ya’ya da jikoki masu yawa.

An haifi Marigayi Sarkin Gaya Alhaji (Dr.) Abdulƙadir Gaya a shekara ta1930, wato 91 da suka wuce kenan, kuma ya kasance tsohon ma’aikacin gwamnati ne tun a zamanin Lardin Arewa. Inda ya yi hidima ga gwamnati na tsahon shekaru.

Mai Martabar yana daga cikin mutanen farko-farko da suka fara aiki a garin Abuja farkon samar da shi wato wajenen shekaru alif ]ari tara da tamanin da wani abu.

Alhaji Abdulƙadir ya fara riƙe sarautar hakimci a garuruwan Ƙunci, da Minjibir.  Kafin daga bisani a naɗa shi Sarkin Gayan a shekarar 1990. A shekarar 2019 ya samu ƙarin ɗaukaka  inda kuma Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya ƙara wa sarautar Gaya girma tare da sauran wasu masarautu guda huɗu a jihar Kano.

Alhaji Abubakar Abduƙadir Gaya ƙani ne ga Marigayin ya bayyana cewa, “kowa ya san marigayin a kan kyautata wa al’umma. Rasuwar margayin ba ƙaramar asara ba ce ga al’umma.”

Marigayin ya kasance ɗaya daga cikin daɗaɗɗun sarakuna a A yankin Arewacin Najeriya.  Kuma ya taimaka ainun wajen kawo zaman lafiya a ɓangarorin Gaya ta Kudu da kuma ta Arewa. Waɗanda kafin zuwan sa mulki ba sa ko ga maciji da Juna.

Shugabanni sun nuna alhini ƙwarai da gaske a kan rasuwar marigayi Kirmau mai Gabas inda Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje da na Jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar da sauransu, sun nuna alhininsu da kuma jajantawa dangane da rasuwar Sarkin, inda Shugaba Buhari ya ambaci marigayin a matsayin ɗaya daga cikin nagartattun sarakunan gargajiya da ake da su a faɗin Nijeriya, waɗanda suka janyo wa harkar sarauta martaba. Sannan daga bisani ya ba wa iyalan mamacin haƙurin rashinsa.

Wani na kusa da Marigayin, Abdurrashid Gaya ya bayyana cewa, Mai martaba sarkin kafin rasuwarsa ya kawo ci gaba marasa ƙirguwa. Inda ya bayyana na farko a matsayin wanda ya taimaka aka samar da ƙarin makarantu a Gaya. Saɓanin yadda a baya suke guda biyu kacal. Sannan kuma ya samar da zaman lafiya a Gaya.

Hakazalika, ya bayyana cewa, yakan ɗauki nauyin marayu da marasa galihu. Sannan kuma duk wani abu nasu na al’ummarsa idan ya taso, yakan shige musu gaba don aiwatar da shi. “Wannan shi ne ake kira da jajirtaccen shugaba,” inji shi.

Allah ya ji ƙan Kirmau mai Gabas ya kyauta makwanci kuma ya dubi bayan da ya bari.