Don ’yan baya Buhari ke cin bashi, inji Gwamnatin Tarayya

*Masu sukar shugaban ba su yi masa adalci ba, cewar Lai Mohammed
*Yar’Adua, Obasanjo da Jonathan suka jefa Najeriya a ƙangin basussuka – Kwamitin Majalisa

Daga AMINA YUSUF ALI

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta kare kanta game da sukar da ta ke fuskanta daga wasu ’yan Nijeriya kan yawan bashin da gwamnatin ke ciyowa a ƙarƙashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari, musamman ma na baya-bayan nan da Shugaban Ƙasar ya aike wa Majalisar Dokoki ta Ƙasa yana neman sahalewarta, don amso rancen zunzurutun kuɗi Dala Biliyan Hu]u da kuma Yuro Miliyan 710 daga ƙasar waje, gwamnatin tana mai cewa, domin gina ’yan baya ne ta ke ta faman haƙilon amso rancen.

Ministan Yaɗa Labarai, Alhaji Lai Mohammed, ne ya bayyana hakan a Alhamis da ta gabata, 23 ga Satumba, 2021, a Maiduguri, Babban Birnin Jihar Borno a wani taron al’umma na gani da ido, wanda ya ƙunshi masu ruwa da tsakin jihar, ciki har da Gwamnan Jihar, Farfesa Babagana Ummara Zulum.

Lai ya ce, manufar amso bashin ita ce, domin aiwatar da ayyukan cigaban ƙasa ta yadda ko bayan Gwamnatin Buhari za a cigaba da cin moriyarsu. Ya ce, Buhari ba zai maso bashi, don kawai ya biya albashi ba, a’a, zai maso ne saboda ya aiwatar da manyan ayyukan raya ƙasa, waɗanda za su cigaba da wanzuwa har illa ma sha Allahu.

Ya ƙara da cewa, “masu sukar Buhari bisa amso bashin nan, ba su yi ma sa adalci ba kuma ba su da gaskiya,” yana mai cigaba da furucin, “a yau layin dogo tsakanin Legas da Ibadan da na Abuja zuwa Kaduna suna tafiya lafiya lumui. A yau mu na da sababbin sauka da tashi a filayen jiragen saman Abuja, Kano, Legas da Fatakwal. A yau layin dogon da ya tashi daga Warri zuwa Itakpe, wanda aka yi watsi da shi shekara aru-aru, yana aiki.

“A yau, a na aiwatar da gyaran titinan tarayya masu aƙalla tsawon kilomita 13,000, inda wasu ma sake gina su ake yi ɗungurgum. Ana yin aikin hanyoyi a kowacce jiha a yanzu. A yau, an kusa kammala aikin Gadar Neja ta Biyu, wacce gwamnatoci da dama na baya suka kasa ture wa buzu naɗi a kanta. Ayyukan da mu ke yi da rancen kuɗin da mu ke amsowa ba za su ƙirgu ba.”

Sai ya ƙara da cewa, wancan rance na Dala Biliyan Huɗu da kuma na Yoro Miliyan 710 za a amso su ne daga Bankin Duniya, Hukumar Cigaba ta Faransa, Bankin EXIM da IFAD.

Sai dai kuma, ana tsaka da wancan kace-nace ɗin ne dai, sai katsam Sanata Solomon Adeola, Shugaban Kwamatin Majalisar Dattawa Akan Kuɗi, ya zargi tsofaffin Shuwagabannin Najeriya da alhakin tsunduma ƙasar a ƙangin basussuka, yana mai nuni da cewa, ba Gwamnatin Buhari ce ta janyo hakan ba tun tale-tale.

Sanata Adeola ya yi wannan bayani ne, a ranar Larabar da ta gabata, inda ya bayyana cewa, dukkan basussukan da ake bin ƙasar nan a tsakanin shekarun 1999 zuwa 2015 dukkansu su Obasanjo da Jonathan da Yar’Adua ne suka ciyo wa ƙasar lokacin suna kan karagar mulkin ƙasar.

Ɗan majalisar ya zubo waɗannan bayanai ne yayin taron hukumar  rarraba arzikin ƙasa na matsakaicin zango na shekarun 2022 zuwa 2024 wanda aka gudanar ranar Larabar da ta gabata.

Adeola ya yi wannan bayanai ne a matsayin ba da amsa a wata tambaya da aka yi musu shi da mai magana da yawun majalisar Dattawa kuma shugabanta Sanata  Ezrel Tabiowo. Inda aka nemi su yi ƙarin bayani game da ƙorafe-ƙorafen da ‘yan Majalisar dokokin Najeriya suke yi a kan yadda Najeriya ta samu kanta tsundum cikin basussuka.

Wannan bayanan an yi su ne yayin da gamayyar kwamitocin kuɗi na majalisar suke gabatar da rahotanninsu a kan kuɗaɗen cikin gida, da kuma basussukan ƙasashen waje, bankuna da sauran abubuwan da suka shafi harkar kuɗi a Najeriya.

A cewar Otedola, kaso ma fi yawa na bashin da ake bin Najeriya wanda a lalace ya kai Naira Triliyan 33, dukkansa a ƙarƙashin mulkin Shuwagabannin baya aka ciyo su. Tun daga zamanin mulkin soja.

Sannan kuma a cewar sa, kusan dukkan basussukan da Buhari ya fara biya wa ƙasar nan an ciyo su ne a zamanin da PDP take yin mulki a ƙasar nan. Wato lokutan mulkin su Olusegun Obasanjo, Umaru Musa Yar’Adua da kuma Goodluck Jonathan, a tsakanin 1999 zuwa 2015.

Don haka a cewar sa, bashin da ake ta kururuto a kansa daɗaɗe ne yake ta taruwa tun daga lokacin mulkin soja har i zuwa lokacin da aka fara mulkin demokraɗiyya. Don haka ma a daina cewa gwamnatin Buhari ita kaɗai ta ciyo wa ƙasar nan dukkan basussukan da ake bin ta.

Amma duk da haka, Buhari ya biya kusan kwatan basussukan da ake bin ƙasar nan. Saboda ba shi da zaɓi sai ya yi abinda ya dace na biyan basussukan da waɗanda suka gabace shi suka ciyo. Inda a ƙarshe ya ce, ya kamata sauran ‘Yan Majalisu su sani, a cikin kowacce Naira 67 ta bashi da za a biya,  Naira 60 Shugabannin baya su suka ciyo bashinta ba Buhari ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *