Kisan ɗalibar jinya Wendy Achumba ya janyo cece-kuce kan cin zarafin mata

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Mutuwar Wendy Achumba mai shekaru 21, ɗalibar makarantar koyon aikin jinya ta Our Lady Nursing School da ke Umulogho a ƙaramar hukumar Obowo ta jihar Imo, ta haifar da fushi da alhini a tsakanin al’umma. Rahotanni sun nuna cewa an kashe ta ne bayan ta ki amincewa da soyayyar wani matashi da ake zargi da aikata laifin tare da wani abokinsa.

An ce Wendy, wadda ke karatun zama ungozoma, tana zaune ita kadai a gidansu a lokacin da lamarin ya faru, bayan abokan zamanta sun tafi aikin horaswa a asibitoci. Rahotanni sun nuna cewa waɗanda ake zargin sun kutsa cikin ɗakinta da daddare inda suka yi ƙoƙarin yi mata fyaɗe. Bayan ta yi turjiya, an kashe ta tare da yanka mata wuya.

Shugabannin matasa na yankin sun bayyana cewa babban wanda ake zargi, wani mai sana’ar gyaran taya, ya taɓa fuskantar zargin yunƙurin fyaɗe a baya. Bayan gano raunuka a jikinsa da kuma halayensa masu tayar da hankali bayan faruwar lamarin, jami’an tsaro sun kama shi. An ce ya amsa laifin tare da bayyana sunan wanda ya taimaka masa wajen aikata laifin.

Lamarin ya tayar da hankalin al’ummar Umulogho, inda mata da matasa suka gudanar da zanga-zangar neman adalci ga marigayiyar. Haka kuma ɗalibai sun gudanar da tattakin kyandir domin girmama ta. Mahukunta da ƙungiyoyin kare haƙƙin mata sun yi Allah wadai da kisan, tare da kira ga hukumomi da su tabbatar an hukunta waɗanda ke da hannu a wannan ɗanyen aiki.

Iyalan Wendy da al’ummar yankin sun buƙaci a yi adalci cikin gaggawa, yayin da gwamnatin jihar Imo da sauran masu ruwa da tsaki suka yi alƙawarin bin diddigin shari’ar har zuwa lokacin da aka tabbatar da hukunci kan waɗanda ake zargi.

By ukarofi

Leave a Reply