Daga JOHN D. WADA, a Lafiya
Rundunar Tsaron Sama ta Nijeriya, ta kai wata ziyarar ta’aziyya na musamman a jihar Nasarawa don jajantawa gwamnatin jihar da iyalai da ‘yan uwan al’ummar Fulani da suka rasa rayukansu sakamakon wasu bama-bamai da sojojin saman suka sako wa wasu matasan Fulani a kauyen Rukubi dake Karamar Hukumar Doma a jihar a shekarar 2023 da ta gabata.
Idan za a iya tunawa kimanin shekara 1 kenan daidai da afkuwar wannan mummunan al’amarin a jihar.
Da yake bayyana wa Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, makasudin ziyarar tasu, shugaban rundunar tsaron sama na Nijeriya, Iya Mashal Hassan Abubakar, bayan ya jajanta wa gwamnati da iyalan wadanda suka rasa ransu din, ya bayyana cewa tunda farko an umurci jami’an tsaron ne su saki bama-baman a kan wasu da aka za ta ‘yan ta’adda ne dake buya a yankin na Rukubi a jihar, amma daga baya sai aka gano harin ya shafi fararen hula.
A kan haka nema ya sa rundunar ta yi alkawarin gudanar da cikakken bincike cikin lamarin a lokacin.
Hassan Abubakar ya ci gaba da cewa, “A yanzu bayan shekara daya cif kenan, wato bayan rundunar ta kammla bincikenta kana ta gano tabbas harin bama-maban da aka sako ta sama da nufin hallaka ‘yan ta’addan ya shafi fararen hula da ke yankin a lokicin inda mutum 37 cikin su wadanda galibin su al’ummar Fulani ne suka rasu wasu kuma suka samu munanan raunuka.
“Shi ya sa muka ga ya dace mu kawo wannan ziyara don mu jajanta wa gwamnatin jihar nan da iyalan mamacin baki daya mu kuma nemi ahuwa,” in ji shi.
Daga nan, jami’in ya yi amfani da wanna dama inda ya tabbatar wa gwamnan da al’ummar yankin Rukubin da jihar baki daya cewa, a yanzu da aka tabbatar da kuskuren da sauran ire-iren su da suka faru a wasu sassan jihohin kasar nan a baya tuni rundunar ta fara nemo wasu ingantattun hanyoyin inganta ayyukanta don hana aukuwar haka a gaba.
A nasa bangaren, Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, ya gode wa tawagar rundunar tsaron saman dangane da ziyarar inda ya ce ba shakka mummunan lamarin da ya auku a shekarar 2023 ya girgiza shi da sauran al’ummar jihar baki daya.
Gwamna Sule ya kara da cewa, a shirye gwamnatinsa take ta hada hannu da rundunar a koyaushe don tabbatar hakan bai sake faruwa ba, ba ma a jihar kadai ba har ma da kasar nan baki daya. Kana ya yi fatan Allah Ya gafarta wa wadanda lamarin ya shafa.
